GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Khamenei na Iran ya fito fili a karon farko tun bayan yaƙi da Israʼila
Gidan talabijin ɗin ƙasar ya nuna jagoran mai shekaru fiye 80 yana gaishe da mutane, su kuma suna yi masa jinjina a cikin wani masallaci a lokacin da jama'a suke jimamin ranar shahadantar ta Imam Hussini.
Khamenei na Iran ya fito fili a karon farko tun bayan yaƙi da Israʼila
Khamenei, 86, can be seen on stage dressed in black as the crowd before him. / Reuters
6 Yuli 2025

Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana a bainar jama'a karon farko tun bayan ɓarkewar rikicin kwanaki 12 da Isra'ila, inda ya halarci wani bikin addini a Tehran, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.

A cikin wani wani bidiyo da aka nuna a gidan talabijin na gwamnati ranar Asabar, an ga shugaban mai shekaru 86 yana gaisa wa da mutane a wani masallaci, yayin da masu ibada ke bikin tunawa da ranar shahadar Imam Hussein.

Khamenei, wanda aka gani a kan dandamali sanye da baƙaƙen kaya, yana kallon taron jama'a da ke daga hannu sama suna rera, 'Jininmu yana ga shugabanmu!'

Gidan talabijin din na gwamnati ya bayyana cewa an ɗauki wannan bidiyo a Masallacin Imam Khomeini da ke tsakiyar Tehran, wanda aka sanya wa suna don tunawa da wanda ya kafa jamhuriyar.

Khamenei, wanda yake jagoranci tun shekarar 1989, ya yi magana a makon da ya gabata ta cikin wani bidiyo da aka dauka tun da farko, amma bai bayyana a bainar jama'a ba tun kafin Isra'ila ta fara kai hare-haren jiragen sama a ranar 13 ga Yuni.

Bayyanarsa ta ƙarshe a bainar jama'a ita ce kwanaki biyu kafin wannan, lokacin da ya gana da mambobin majalisar dokoki.

Harin na Isra'ila ya biyo bayan dogon lokaci na yakin bayan fage tsakaninta da Iran, wanda aka ce manufarsa ita ce hana Iran samar da makamin nukiliya - wani abu da Tehran ta sha musantawa.

Hare-haren sun kashe fiye da mutane 900 a Iran, kamar yadda ɓangaren sharia’ar ƙasar ya bayyana, yayin da martanin harin makamai na Iran ya kashe akalla mutane 28 a Isra'ila, a cewar alƙaluman hukumomi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us