Wata kotu a Burkina Faso ta ƙaddamar da bincike kan wani saƙon da aka wallafa a shafukan sada zumunta wanda ya yi kira da a “kashe” Fulani, wadda ƙabila ce da ake yawan hantara a yankin Sahel.
Mai shigar da ƙara a kotun Ouagadougou Blaise Bazie a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis da yammaci, ya bayyana cewa hukumomi na gudanar da bincike kan mutanen da suka wallafa ko kuma taimakawa wurin yaɗa saƙon kiran da aka yi na “kashe jama’ar wata ƙabila” a shafin Facebook.
Ya bayyana cewa wasu a shafukan sada zumunta na wallafa cewa “waɗannan mutanen ‘yan ta’adda ne waɗanda ke jawo ƙunci” a cikin ƙasa.
Sai dai mai shigar da ƙarar bai kama sunan wata ƙabila ba, duk da cewa akasarin saƙonnin sun shafi al’ummar Fulani.
Fulani makiyaya na yawan fuskantar hantara a yankin Sahel, inda ake zarginsu da haɗa kai da masu iƙirarin jihadi da zama mayaƙansu.
“Ana gudanar da bincike da niyyar kama waɗanda suka yi wannan kiran,” in ji Bazie
"Waɗannan saƙonnin, waɗanda maganganu ne da ke tunzura jama’a domin tayar da tarzoma, sun zama babbar barazana ga zaman lafiya da haɗin kan jama'a," in ji shi, inda ya ƙara da cewa akwai yiwuwar waɗanda suka wallafa saƙonnin su je kurkuku.
Burkina Faso na fama da rikici tun daga 2015, lamarin da ya haddasa mutuwar fiye da mutum 26,000, rabinsu sun mutu ne bayan juyin mulkin d aka yi a 2022, kamar yadda Acled ta bayyana, wadda ƙungiya ce da ke tattara bayanai game da adadin waɗanda suka mutu sakamakon rikici a faɗin duniya.