AFIRKA
4 minti karatu
‘Yan adawan Sudan ta Kudu sun koka kan hare-hare yayin da Amurka ke gargaɗi kan ƙaruwar yaƙi
Arangama tsakanin dakaru masu alaƙa da Shugaba Salva Kiir da daɗaɗɗen abokin adawarsa, Mataimakin shugaban ƙasar na farko Riek Machar, na barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyarsu ta 2018 tare da barazanar jefa ƙasar cikin yaƙin basasa
‘Yan adawan Sudan ta Kudu sun koka kan hare-hare yayin da Amurka ke gargaɗi kan ƙaruwar yaƙi
Sudan ce ƙasar da ta fi ko ƙarancin shekaru a duniya bayan ta samu ‘yancin kanta a shekarar 2011 / AFP
25 Maris 2025

‘Yan adawan Sudan ta Kudu sun ce an yi luguden wuta a ɗaya daga cikin sansanonin sojojinsu kusa da babban birnin ƙasar Juba ranar Litinin da maraice  yayin da Washington ke gargaɗin cewa "ta damu matuƙa " game da  ƙaruwar yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu da ke adawa da juna.

Arangama tsakanin dakaru masu alaƙa da Shugaba Salva Kiir da kuma daɗaɗɗen abokin adawansa, Mataimakin shugaban ƙasar na farko Riek Machar, na ƙara barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyarsu ta shekarar 2018 tare da barazanar tsunduma ƙasar cikin yaƙin basasa.

Da maraicen ranar Litinin, jam’iyyar Machar, Sudan People's Liberation Movement mai adawa, ta ce an kai hari a sansanin sojinta a Wunaliet, mai nisan kimanin kilomita 15 (mil tara) daga babban birnin ƙasar Juba.

"Wannan matakin tsokana ya keta (yarjejeniyar zaman lafiyar shekarar 2018)," in ji wani mai magana da yawun jam’iyyar a wata sanarwa.

Daga farko dai, wani mai magana da yawun soji mai alaƙa da Kiir, Lul Ruai Koang, ya yi gargaɗin cewa dakarun Machar a wuraren na "ƙara kai komonsu " tare da tura  ‘yan sintiri zuwa yankuna da sojoji suke "a wani yanayi na soji".

Rundunar soji dai ba ta tabbatar da hare-haren na baya baya ba, amma rahotanni daga ƙasar sun ce hare-haren sun ƙunshi "ruwan bama-bamai ".

Sudan ta Kudu ita ce ƙasar da ta fi ko wace ƙasa ƙarancin shekaru a duniya, bayan ta samu ‘yancin kanta a shekarar 2011.

Bayan haka, ta tsunduma cikin yaƙin basasa na shekara biyar tsakanin Kiir da Machar da ya kashe mutum 400,000 zuwa lokacin da aka yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018 ta kawo gwamnatin haɗin-kai.

'Tangal-tangal a baki'

Arangamar baya-bayan nan ta fi faruwa ne ƙaramar hukumar Nasir da ke jihar Upper Nile da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Wasu ‘yan bindiga da ake kira White Army, masu alaƙa da Machar, sun karɓe iko da wani sansanin soji a Nasir a farkon watan Maris.

Rundunar sojin ta mayar da martani da hare-haren sama a wuraren da ke kusa, ciki har da bama-bamai masu sinadari mai saurin kamawa da wuta da ke ƙara wuta lokacin fashewa, in ji wata sanarwar da Nicholas Haysom, shugaban rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Sudan ta Kudu (UNMISS) ranar Litinin.

"Waɗannan hare-haren kan mai uwa da wabi a kan fararen hula suna janyo mace-mace da rauni mai muni, musamman ƙuna," in ji Haysom, yana mai ƙarawa da cewa an raba kimanin mutum 63,000 da gidajensu.

Haysom ya ce ƙasar tana "tangal-tangal a bakin sake faɗawa a rijiyar yaƙin basasa ".

Masharhanta sun ce Kiir ya ƙasance yana ɗaukar matakai a watannin nan domin tura Machar gefe, ya kuma ƙara wa sabbin mambobi girma zuwa cikin majalisar ministoci  ba tare da  neman shawara ba yayin da mai shekara 73 ke shirya yadda za a gaje shi.

A makon da ya gabata, ya maye gurbin gwamnan Upper Nile mai alaƙa da Machar da ɗaya daga cikin mutanensa.

Jam’iyyar Machar ta ce an kama 22 daga cikin mambobin jam’iyya da na sojinta tun watan Fabrairun, ciki har da ministan ma fetur, Puot Kang Chol da kuma mataimakin hafsan sojoji, Janar Gabriel Duop Lam.

Ranar Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce dole Kiir da Machar "su tattauna kai tsaye domin kauce wa taɓarɓarewar rikici a Sudan ta Kudu ".

"Hare-haren ‘yan bindiga mara alaƙa da gwamnati da hare-haren sama na gwamnatin da kuma ƙara wa jami’ai da aka kama da laifi girma ababe ne masu sa damuwa sosai," kamar yadda ta bayya a wata sanawar da ta wallafa a shafin X.

Ƙasar Sudan ta Kudu ɗaya ce daga cikin ƙasashen da suka fi talauci a duniya, kuma asusun kula da ƙananan yara ta MDD (UNICEF) a ranar Litinin ta ce ƙasar tana fama annobar kwalara mafi muni da ta taɓa gani tun da ta sami ‘yancin kai, inda kusan kumtum 700 suka mutu cikin wata shida, ciki har da ƙananan yara da yawa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us