Sanarwar da aka yi ta Kotun Gaza ta Sarajevo, "kotun mutane" da aka kafa a matsayin wani shiri mai zaman kansa don bincika laifukan yaiƙ da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza, ta yi Allah wadai da "gwamnatin" Isra'ila da ayyukanta, a ranar Alhamis.
A cikin kwanaki ukun da suka gabata, an gudanar da taruka a Jami'ar Ƙasa da Ƙasa ta Sarajevo ta Tattalin Arziki da Siyasa, kan kisan kiyashi da lalata Gaza, da laifin yunwatarwa, da rawar da tsarin kasa da kasa ke takawa a zamanin kisan kare dangi, da kuma laifuntar da zanga-zangar ɗalibai.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa fiye da 54,000 galibi mata da kananan yara a Gaza tun daga watan Oktoban 2023. Hare-haren bama-bamai da ba a saba gani ba ya ɗaiɗaita kusan ɗaukacin yankin tare da haifar da ƙarancin abinci da sauran kayan masarufi, lamarin da ke kara barazanar yunwa.
Sanarwar Sarajevo ta bayyana "ɓacin rai game da ci gaba da kisan kiyashi a Falasɗinu" inda suke yin "aiki tare da abokan hulɗa a faɗin duniya don kawo ƙarshen kisan kiyashi da kuma tabbatar da ɗaukar mataki kan masu aikata laifuka da masu ba da izinin hakan" don "samun ‘yancin Falasɗinu."
"Muna Allah wadai da gwamnatin Isra'ila, da aikata kisan kiyashi, da manufofinta na tsawon shekaru mulkin mallaka na kama-wuri-zauna da wariyar launin fata da zalunci da kafa matsugunan da ba bisa ka'ida ba, da hana 'yancin dawowa da azabtar da jama'a da tsare jama'a da azabtarwa da zalunci da kisa da cin zarafi ta hanyar lalata, da rushe wurare da tilasta wa jama’a barin muhallansu, da hana su duk wasu damarmaki na tattalin arziƙi,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta sanar da ƙin amincewa da "aƙidar Yahudanci ta tsatsauran ra’ayi, a matsayin aƙidar hukuma ta gwamnatin ƙasar Isra'ila, ta sojojin da suka yi wa Falasɗinu mulkin mallaka da kafa kasar Isra'ila ɓaraguzanta, da ƙungiyoyi da masu goyon bayan Isra'ila a yau."
Don haka, sanarwar ta yi kira "domin kawo ƙarshen mulkin mallaka a faɗin kasar, da kawo karshen tsarin mulkin ƙabilanci, da kuma maye gurbin aƙidar Yahudanci ta tsatsauran ra’ayi da tsarin bisa kan daidaitattun 'yancin ɗan adam ga Kiristoci, Musulmai, Yahudawa, da sauransu".