Iran ta bayyana cewa tana son fadada dangantakarta da Saudiyya a dukkan fannoni.
Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wani saƙo da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya aika wa takwaransa na Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, a ranar Laraba.
A cewar gidan talabijin na gwamnati a Iran, jakadan Iran a Riyadh, Alireza Enayati ne ya mika saƙon ga Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Waleed bin Abdulkarim Al-Khereiji.
Saƙon ya mayar da hankali kan “bunkasa da ƙarfafa dangantaka a dukkan fannoni,” in ji gidan talabijin ɗin.
An sake farfaɗo da wakilcin diflomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya a watan Satumban 2023, bayan shekaru bakwai da katsewar dangantaka tun 2016.
Saudiyya da Iran sun sanar da dawo da dangantakar diflomasiyya a ranar 10 ga Maris na 2023, bayan tattaunawar da China ta jagoranta a birnin Beijing.
Riyadh ta katse dangantaka da Tehran a 2016 bayan hare-haren da aka kai kan ofishin jakadancinta a babban birnin Iran da kuma ofishin jakadancinta a birnin Mashhad na arewa maso gabas.
Hare-haren sun biyo bayan kisan fitaccen malamin Shia, Sheikh Nimr al-Nimr, wanda aka yanke wa hukunci kan “laifukan da suka shafi ta’addanci.”