AFIRKA
2 minti karatu
Mutum fiye da 1,300 sun kamu da cutar kwalara a cikin kwana guda a Sudan
Ko a ranar Laraba sai da ma’aikatar lafiya ta Jihar Khartoum ta sanar da samun mutum 942 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutum 25 a ranar Talata, yayin da a ranar Litinin aka samu mutum 1,177 da suka kamu da cutar da mutuwar mutum 25.
Mutum fiye da 1,300 sun kamu da cutar kwalara a cikin kwana guda a Sudan
A watan Agustan 2024, hukumomin Sudan sun ayyana cutar kwalara a matsayin annoba ta kasa. / Reuters
30 Mayu 2025

Hukumomin Sudan a ranar Alhamis sun sanar da ƙaruwar cutar kwalara a Jihar Khartoum.

“An samu ƙaruwa a adadin waɗanda suka kamu da kwalara a jihar inda aka samu mutum 1,375 a ranar Laraba,” in ji Mohammed Al-Tijani, daraktan hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Ma’aikatar Lafiya ta Khartoum.

“Adadin mutanen da ke mutuwa ya ragu taimakon likitoci, inda aka samu asarar rayuka 23 a ranar Laraba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Ya bayyana cewa a halin yanzu akwai marasa lafiya 1,116 da ake kula da lafiyarsu a wuraren killace marasa lafiya.

“An buɗe wuraren killace marasa lafiya da kuma samar matsugunai huɗu a wuraren da ake samun yawan cututtuka, inda ake sa ran gano cututtukan a cikin sauri da magance su da kuma rage mace-macen,” in ji Al-Tijani.

Ko a ranar Laraba sai da ma’aikatar lafiya ta Jihar Khartoum ta sanar da samun mutum 942 da suka kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutum 25 a ranar Talata, yayin da a ranar Litinin aka samu mutum 1,177 da suka kamu da cutar tare da mutuwar mutane 45.

Bisa ƙididdigar da gwamnatin kasar ta fitar, an samu jimillar mutane 60,993 da suka kamu da cutar kwalara a Sudan, waɗanda suka hada da mutuwar mutane 1,632.

A watan Agustan 2024, hukumomin Sudan sun ayyana cutar kwalara a matsayin annoba ta kasa.

Ɓangaren kiwon lafiya na kasar Sudan na ɗaya daga cikin ɓangarorin da yaƙin basasar da ake ci gaba da yi tsakanin sojojin kasar Sudan da kuma abokan hamayyarta na kungiyar agajin gaggawa ta RSF ya ɗaiɗaita, wanda ke faruwa tun daga watan Afrilun shekarar 2023.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us