DUNIYA
2 minti karatu
A karon farko an amince da amfani da maganin malaria na yara da jaririai
Ana iya narka maganin har a cikin ruwan nono, kuma yana da dandanom dan itacen cherry mai dadi don saukaka ba wa yara da jariran.
A karon farko an amince da amfani da maganin malaria na yara da jaririai
Malaria na kashe mutane da dama Afirka inda yara da jarirai suka fi illatuwa daga cutar. / Reuters
8 Yuli 2025

A ranar Talata Novartis ya ce ya samu amincewa a Switzerland don amfani da Coartem Baby, wanda suka ce shi ne maganin cutar zazzaɓin cizon sauro da aka samar saboda jarirai da yara ƙanana.

Kasashen Afirka takwas da suka shiga aikin gwajin na shirin bayar da amincewarsu don amfani da maganin, wanda ake kuma kira da Riamet Baby a wasu kasashen.

Kimanin jarirai miliyan 30 ake haifa a kowace shekara a yankunan Afirka da ke fuskantar hatsarin kamuwa da cutar malaria, inda wani bincike da aka gudanar a Yammacin Afirka ya ce kashi 3.4 zuwa 18.4 na yara ‘yan kasa da shekaru shida na kamuwa da cutar, in ji Novartis.

Norvatis ya kaddamar da Coartem don magance cutar malaria a 1999, a yanzu kuma ya kawo sabon maganin don amfanin jarirai da yara kanana.

Ana iya narka maganin har a cikin ruwan nono, kuma yana da dandanon ɗan itacen cherry mai daɗi don sauƙaƙa bai wa yara da jariran.

Har ya zuwa yanzu, babu maganin malaria da aka amince a yi amfani da shi ga jarirai da nauyinsu yake kasa da kilo 4.5.

Kasashen takwas da suka shiga aikin gwajin maganin su ne Burkina Faso da Cote d’Ivoire da Kenya da Malawi da Mozambique da Nijeriya da Tanzania da Uganda.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us