DUNIYA
1 minti karatu
'Yan sanda sun kama wani mutum bisa zarginsa da ƙona Ƙur'ani a masallaci a Faransa
An tsare mutumin da ake zargin kuma yana fuskantar tuhumar 'yan sanda, kamar yadda ofishin babban mai shigar da ƙara na Lyon ya tababbatar.
'Yan sanda sun kama wani mutum bisa zarginsa da ƙona Ƙur'ani a masallaci a Faransa
The incident occurred early on Monday morning, shortly before 4 am local time, at the Errahma Mosque as it was opening for morning prayers. / AA
4 Yuni 2025

An kama wani mutum a ranar Talata, wanda ake zargi da ƙona Ƙur'ani a cikin wani masallaci da ke Villeurbanne a kusa da garin Lyon a Faransa, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

An bayyana mutumin a matsayin wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa, kamar yadda mai gabatar da ƙara da kuma wata majiya daga 'yan sanda suka bayyana.

Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin, kafin ƙarfe huɗu na safe a Masallacin Errahma yayin da ake buɗe masallacin don Sallar Asuba.

Ana zargin wanda ake tuhuma ya shiga masallacin da niyyar yin sata, sannan sai ya ƙona wani kwafi na Alƙur'ani kafin ya tsere daga wurin.

Shugabannin masallacin, tare da magajin garin Villeurbanne, Cedric Van Styvendael, sun yi Allah wadai da wannan aiki, suna bayyana shi a matsayin "mummunan hari na ƙiyayya ga Musulunci."

"Wannan cin zarafi ne da ba za a amince da shi ba, kuma muna kira da a tabbatar da adalci," in ji shugabannin masallacin a cikin wata sanarwa.

Babu wata sanarwa daga jami'an gwamnati da ta yi Allah wadai da wannan aiki.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us