Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga ƙasar Mali, abin da ya kawo ƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan ƙasa ta Yammacin Afirka.
“Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare ƙasarsu. Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a ƙasar,” in ji kungiyar a ranar Juma’a.
“Mun kashe dubban ‘yan ta’adda da shugabanninsu waɗanda suka daɗe suna cuzguna wa fararen hula,” a cewar kungiyar.
Mali, wata ƙasa da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012.
Rundunar Afrika ta Rasha za ta maye gurbin Wagner
Sojojin mulkin ƙasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulɗa.
Rahotanni sun nuna cewa duk da sanarwar Wagner, Rasha za ta ci gaba da kasancewa a ƙasar ta Yammacin Afirka, tare da Rundunar Afrika, wata rundunar sojojin haya da gwamnatin Rasha ke kula da ita.
Tun da farko a wannan shekarar, Mali, Burkina Faso da Nijar, ƙasashe uku da ke ƙarƙashin mulkin soja, sun fice daga ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka.
Sun kafa wata sabuwar ƙungiya mai suna Ƙungiyar Ƙasashen Sahel AES.