Za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar nukiliya tsakanin Amurka da Iran a ranar Lahadi a birnin Muscat, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Oman ya sanar a ranar Alhamis, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada cewa ba za a bari Tehran ta mallaki makamin nukiliya ba.
"Ina farin cikin tabbatar da cewa za a gudanar da zagaye na shida na tattaunawar Iran da Amurka a Muscat a wannan Lahadin mai zuwa," in ji Minista Badr Albusaidi a wani sakon da ya wallafa a X.
Tun daga watan Afrilu, Tehran da Washington sun gudanar da zagaye biyar na tattaunawa don cim ma sabuwar yarjejeniyar nukiliya da za ta maye gurbin yarjejeniyar 2015 da Trump ya janye daga ita a wa’adin mulkinsa na farko a 2018.
Sanarwar daga Oman ta zo ne sa’o’i kadan bayan da Shugaba Donald Trump ya ce ana kwashe ma’aikatan Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya mai yiwuwa saboda fargabar “rikicin da ke ruruwa” a yankin.
An ruwaito a baya cewa Amurka na shirin kwashe wasu daga ma’aikatanta a ofisoshin jakadancinta a Iraƙi da Bahrain da Kuwait.
Rahotanni sun nuna cewa yiwuwar kwashe ma’aikata ya haifar da karin farashin mai da ya kai sama da kashi 4 cikin 100 kafin farashin ya sauka a ranar Alhamis.
Kamfanonin makamashi na kasashen waje suna ci gaba da ayyukansu kamar yadda aka saba, in ji wani babban jami’in Iraki da ke kula da ayyukan a filayen mai na kudu a wata hira da Reuters a ranar Alhamis.
Wani jami’in Amurka ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje ta ba da izinin tafiya ga wadanda suka zabi barin Bahrain da Kuwait.
Trump ya kuma sake jaddada cewa ba zai bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, yayin da ake ta hasashen cewa Isra’ila na iya kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Iran ta yi barazanar kai hari kan sansanonin sojin Amurka a yankin idan rikici ya barke. Trump, wanda a baya ya nuna ƙwarin gwiwa kan tattaunawar, a wata hira da aka buga a ranar Laraba ya ce yanzu "ƙwarin gwiwarsa ta ragu" kan cim ma yarjejeniya.
Tun dawowarsa ofis a watan Janairu, Trump ya farfado da yakin "matsin lamba mafi girma" kan Tehran, yana goyon bayan tattaunawar nukiliya amma yana gargadin daukar matakin soja idan ta gaza.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta sabunta shawarar tafiye-tafiye ta duniya a ranar Laraba da daddare don nuna sabon matsayi na Amurka.
"A ranar 11 ga Yuni, Ma’aikatar Harkokin Waje ta umarci ficewar ma’aikatan gwamnati na Amurka wadanda ba na gaggawa ba saboda karuwar tashin hankali a yankin," in ji sanarwar.
Wani babban jami’in tsaro na Iran ya shaida wa Press TV na Iran a ranar Alhamis cewa ficewar iyalan sojojin Amurka ba ya nufin barazana.
A ranar Laraba, Ministan Tsaron Iran ya gargadi Washington cewa Tehran za ta kai hari kan sansanonin Amurka a yankin idan aka jawo ta cikin yaki idan tattaunawar nukiliya ta gaza.
Amurka na da sansanonin soja a fadin yankin Gabas ta Tsakiya mai arzikin mai, ciki har da Iraƙi, Kuwait, Qatar, Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Hukumar kula da harkokin ruwa ta Birtaniya ta gargadi cewa karuwar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya na iya haifar da karin ayyukan soja da za su iya shafar jigilar kaya a manyan hanyoyin ruwa.