AFIRKA
6 minti karatu
Ƙasashe 20 mafiya karfin soji a Afirka
Masar da Aljeriya da Nijeriya su ne suke da sojoji mafiya karfi a Afirka zuwa watan Yunin 2025, kamar yadda Alƙaluman Karfin Soji na Duniya na 2025 ya nuna.
Ƙasashe 20 mafiya karfin soji a Afirka
South Africa's military is among the strongest in Africa. / Photo: AFP
20 Yuni 2025

Masar, da Aljeriya da Nijeriya su ne kan gaba a wajen ƙarfin soja a nahiyar Afirka a watan Yunin shekarar 2025, kamar yadda rahoton Global Firepower Index na 2025 ya nuna.

Rahoton ya yi la’akari da karfin sojojin ƙasashe daban-daban bisa adadin soja, da matakin horonsu, da karfin rundunar sama wanda ya haɗa da adadin jiragen yaƙi da tsarin jiragen sama.

Haka kuma, ana auna karfin sojojin bisa kayan yaki na kasa, wanda ya haɗa da motocin yaƙi, da tankokin soja, da bindigogin harba roka da sauran kayan aiki.

Masar tana da sojoji miliyan 1.2

Ga ƙasashen da suke da manyan tekuna, karfin sojojin ruwa ma ana la’akari da shi. Wannan ya haɗa da jiragen yaƙi na ruwa, da jiragen ƙarkashin ruwa, da kayan sintiri na ruwa da sauran fasahohin ruwa.

Matsayin tattalin arzikin ƙasa da kuma kasafin kuɗin da aka ware wa sojoji shi ma wani muhimmin abu ne da rahoton Global Firepower ya yi amfani da shi wajen tantance ƙarfin sojojin Afirka.

Masar, wadda take da karfin soja mafi girma a nahiyar, tana da sojoji miliyan 1.2, inda 440,000 daga cikinsu ke aikin kai-tsaye a fagen fama.

Kasar da ke arewacin Afirka mai yawan mutane miliyan 115 tana da sojoji ƙasa 685,000, da sojojin sama 50,000 da kuma na ruwa 32,500.

Haka kuma, Masar tana da sojoji 480,000 a matsayin na ko ta kwana, da kuma 300,000 a ɓangaren wasau dakarun na musamman.

Ƙarfin sojojin Masar ya haɗa da motocin yaki a ƙasa fiye da 41,000, da tankokin soja fiye da 3,600, da bindigogin harba roka 960, da kuma bindigogin atilare fiye da 1,000.

A ɓangaren sama kuma, Masar tana da jirage fiye da 1,000, ciki har da jiragen yaki 238, da jiragen daukar kaya 348, da kuma jiragen horarwa 345.

A ɓangaren ruwa, Masar tana da kayan aiki masu yawa, ciki har da jiragen ƙarkashin ruwa guda takwas da jiragen daukar jiragen sama guda biyu masu iya daukar kaya har ton 236,000.

Aljeriya ce a matsayi na biyu da sojoji 610,000

Aljeriya, wadda take matsayi na biyu a Afirka, tana da jimillar sojoji 610,000, inda 325,000 daga cikinsu ke aiki kai-tsaye.

Aljeriya tana da sojojin ƙasa 182,500, yayin da rundunar sama ke da sojoji 14,000, sai kuma rundunar ruwa da ke da 6,000.

A ɓangaren sauran masu kayan sarki na musamman, Aljeriya tana da 150,000 a kasar dake da yawan mutane miliyan 46.

Ƙarfin Aljeriya a ƙasa

Karfin Aljeriya a kasa ya haɗa da motocin yaki 26,000, da tankokin soja kusan 1,500, da bindigogin atilare masu sarrafa kansu 224, da kuma bindigogin harba roka sama da 480.

A ɓangaren sojojin sama, Aljeriya tana da jiragen sama 608, ciki har da jiragen yaki 102, da jiragen horo 87, da jiragen ɗaukan kaya 299, da kuma jiragen musamman guda 10.

Najeriya tana matsayi na uku da sojoji 280,000.

Najeriya, wadda take matsayi na uku a Afirka, tana da jumillar sojoji 280,000, inda 230,000 daga cikinsu ke aiki kai-tsaye.

Sojojin ƙasa na Najeriya sun kai 65,000, yayin da rundunar sama ke da 15,000, sai kuma rundunar ruwa da ke da 5,500.

Najeriya tana da sauran masu kayan sarki kusan 50,000.

A ƙasa, Najeriya tana da motocin yaki 8,962, da tankokin soja 330, da bindigogin atilare masu sarrafa kansu 40, da kuma bindigogin harba roka 339.

A bangaren sama, Najeriya tana da jiragen sama 163, ciki har da jiragen yaki 14, da jiragen ɗaukar kaya 66, da jirage na musamman 11, da kuma jiragen bayar da horo 28.

Rundunar ruwa ta Najeriya tana da jiragen sintiri 109.

Afirka ta Kudu tana matsayi na hudu da sojoji 151,000.

Afirka ta Kudu tana da sojojin kasa 62,800, da sojojin sama 13,815, da rundunar ruwa kuma tana da kusan 7,900. Haka kuma, tana da sauran masu kayan sarki kusan 50,000.

A kasa, Afirka ta Kudu tana da motocin yaki 18,692, da tankokin soja 252, da bindigogin atilare masu sarrafa kansu, bindigogin harba roka 101, da kuma bindigogin harba harsashi 134.

A bangaren sama, kasar dake da mutane miliyan 63 tana da jiragen sama 182, ciki har da jiragen daukar kaya 87, jiragen koyarwa 81, da kuma jiragen yaki guda biyu.

Rundunar ruwa ta Afirka ta Kudu tana da jiragen karkashin ruwa guda uku, jiragen sintiri 33, da kuma jiragen yaki na ruwa guda biyu.

Habasha ce ƙasa cikon ta biyar mafiya ƙarfi

Habasha tana matsayi na biyar da sojoji 162,000.

Habasha tana da sojojin kasa 75,000, rundunar ruwa tana da sojoji 10,000, rundunar sama 5,000.

A kasa, Habasha tana da motocin yaki 7,300, da tankokin soja 338, bindigogi masu sarrafa kansu 35, bindigogin harba roka 40, da kuma bindigogin harba manyan harsasai 309.

A bangaren sama, ƙasar dake da mutane miliyan 129 tana da jiragen sama 103, ciki har da jiragen ɗaukar kaya 33, da jiragen horarwa 34, da kuma jiragen yaki 25.

DRC da Sudan suna cikin manyan ƙasashe goma.

Angola, da Maroko, da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, da Sudan da Libya suna cikin jerin kasashe goma mafi karfi a Afirka.

Sauran ƙasashe da suka shiga jerin kasashe ashirin mafiya ƙarfi a Afirka sun haɗa da Kenya, da Chadi, da Mozambique, da Tunisiya, da Tanzaniya, da Kamaru, da Côte d'Ivoire, da Mali, da Zambiya da kuma Ghana.

Daga cikin ƙasashe da suka fi rauni a ɓangaren soja a Afirka akwai Benin, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Somaliya, da Saliyo da Laberiya.

Ga jerin kasashen Afirka daga mafi ƙarfi zuwa mafi rauni bisa bayanan Global Firepower Index na 2025:

  • 1. Masar

  • 2. Aljeriya

  • 3. Nijeriya

  • 4. Afirka ta Kudu

  • 5. Habasha

  • 6. Angola

  • 7. Maroko

  • 8. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

  • 9. Sudan

  • 10. Libya

Rahoton na Global Firepower ya bayyana cewa yana amfani da abubuwa fiye da 60 wajen tantance karfin sojojin kasashe.

'Unbiased look' into military strength

The Global Firepower, which tracks defence-related information of 145 countries globally, says that it "makes use of over 60 factors in our in-house formula to determine a given nation's power index."

The US-based organisation further says that its ranking "allows smaller, more technologically-advanced nations to compete with larger, lesser-developed ones."

To level the playing field, the Global Firepower says: "Some bonuses and penalties are added for refinement that, in the end, we hope presents an unbiased look into the potential conventional military strength of a world power."

In Africa, the Global Firepower analysed 38 out of the continent's 54 countries, with no explanation given on the omission of some 16 countries, including The Gambia, Togo and Malawi.

'Rashin nuna fifiko' wajen auna ƙarfin na soja

Kungiyar Global Firepower, wacce ke bin diddigin bayanan da suka shafi tsaro na kasashe 145 a duniya, ta ce tana amfani da abubuwa sama da 60 a tsarin cikin gida don tantance ma'aunin ƙarfin soja na ƙasa.

Kungiyar da ke Amurka ta ci gaba da cewa ma’aunin nata na bai wa ƙananan kasashe da suka ci-gaba ta fannin fasaha damar yin gogayya da manyan ƙasashe da ke da ƙarancin fasaha.

A nahiyar Afirka, kungiyar Global Firepower ta yi nazari kan kasashe 38 daga cikin 54 na nahiyar, ba tare da bayar da wani bayani kan cire wasu ƙasashe 16 da suka haɗa da Gambia da Togo da Malawi ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us