Wani jirgin saman fasinja na Air India ɗauke da mutum 242 ya yi hatsari a Ahmedabad, babban birnin jihar Gujarat da ke yammacin Indiya, kamar yadda kafafen yada labarai da dama suka ruwaito.
A cewar rahoton, jirgin AI171 ya tashi ne daga Ahmedabad zuwa filin jirgin sama na Gatwick na Landan a lokacin da hatsarin ya faru.
Jirgin ya fado ne a ginin ɗakunan kwanan likitoci jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Sardar Vallabhbhai Patel da ke Ahmedabad a ranar Alhamis, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
Kamfanin Air India ya ce fasinjojin da ke cikin jirgin da ya yi hatsarin sun hada da 'yan kasar Indiya 169, 'yan Burtaniya 53, da 'yan Portugal 7, da 'yan kasar Canada daya, matukan jirgi biyu da ma'aikatan cikin jirgi goma.
Kamfanin Air India ya fitar da wata takaitacciyar sanarwa ga manema labarai yana mai cewa "A halin yanzu, muna kan tantance cikakkun bayanai kuma za mu fitar da sakamakon abin da muka tattara da wuri."
Shugaban kamfanin jiragen Air India, N. Chandrasekaran ya bayyana "matuƙar baƙin cikinsa" kan hatsarin.
“Babban abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne tallafa wa duk mutanen da abin ya shafa da iyalansu,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
"Muna yin duk abin da za mu iya don taimaka wa kungiyoyin bayar da agajin gaggawa a wurin da kuma ba da duk goyon baya da kulawa."
A cewar rahotannin farko, jirgin ya faɗi ne a kusa da yankin Meghani Nagar na birnin, inda bidiyon yadda abin ya faru da ke yawo a shafukan sada zumunta suka nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe daga wurin da hatsarin ya auku.
Jirgin ya tashi ne da karfe 1:38 na safe agogon kasar ya kuma fada cikin wani gini kusa da filin jirgin saman Ahmedabad da karfe 1:40 na rana.
Jami’an filin jiragen sama na Gatwick sun ce jirgin ya kamata ya sauka a birnin Landan da karfe 6.25 na yamma agogon kasar.
Hukumomin kasar sun kaddamar da aikin ceto, kuma jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.
Yayin da bayanai ake ci gaba da samun taƙaitattun bayanai, majiyoyi sun nuna cewa fasinjoji da ma’aikatan jirgin na ciki a lokacin da hatsarin ya afku.
Ana sa ran jami’an hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama (DGCA) za su gudanar da cikakken bincike kan musabbabin hatsarin.
Shaidu da ke kusa da filin jirgin sun ce sun ji ƙarar fashewar wani abu mai ƙarfi kafin daga bisani jirgin ya faɗi.
Gwamnatin Gujarat ta ba da tabbacin daukar matakin gaggawa tare da tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.
"Mun yi matuƙar kaɗuwa da jin labarin lamarin jirgin AirIndia na Ahmedabad-London a kusa da filin jirgin saman Ahmedabad," in ji Yusuf Pathan, tsohon dan wasan cricket kuma dan majalisar dokokin Indiya, a shafin X.