AFIRKA
1 minti karatu
Labaranmu Na Yau, 8 ga watan Mayun 2025
Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da dama a Jihar Borno sannan za a ji cewa mayaƙan RSF sun ƙaddamar da sabbin hare-hare a gabashi da kudancin Sudan
Labaranmu Na Yau, 22 ga watan Afrilun 2025 / TRT Afrika Hausa
8 Mayu 2025

Pakistan ta harbo jiragen Indiya yayin da tashe-tashe hankula ke kara kamari a tsakaninsu

A wani yunkuri na yayyafa ruwa a rikicin da ya barke tsakanin Indiya da Pakistan wadanda ke gaba da juna, shugabannin kasashen duniya sun bukaci su daina fada.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga kasashen biyu da su tsagaita wuta, yayin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ba da goyon bayan diflomasiyya don kawo karshen tarzoman.

Pakistan ta ce harin da Indiya ta kai ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 31 da kuma jikkata wasu 57, inda ta kuduri aniyar mayar da martani.

Kazalika, ta ce dakarunta na sama sun kakkabo jiragen yakin Indiya guda biyar da wani mara matuki daya a wani mataki na "kare kai".

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us