Kasuwanci
8 minti karatu
Tabbatacciyar hanyar samar da kuɗaɗe: Tubalin fafutukar Tarayyar Afirka kan neman adalci da daidaito
Tsare-tsaren tattalin arzikin da ya dawwamar da rashin dogaro da kai da Afrika ba ta yi kan kuɗi, su ma wasu nau'ikan rashin adalci ne, da ke buƙatar kulawa kamar irin wacce aka bai wa kurakuren da aka tafka bisa tarihi da Babban Taron Tarayyar Afrik
Tabbatacciyar hanyar samar da kuɗaɗe: Tubalin fafutukar Tarayyar Afirka kan neman adalci da daidaito
Dalar Amurka
March 4, 2025

Daga Mubarak Aliyu

Neman adalci da daidaito shi ne jigon agendar siyasar Tarayyar Afrika (AU), musamman biyo bayan kiraye kiraye kan biyan diyyar rashin adalcin da aka tafka a tarihance.

Sai dai, cim ma waɗannan ƙudurorin ya dogara ne kan magance ƙalubalen tsare tsaren tattalin arzikin da ke ci gaba da kawo wa cigaban nahiyar tasgaro.

Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ƙasashen Afrika ke fuskanta ita ce rashin tabbatarciyar hanyar samar da kuɗaɗe wacce ta siffantu da hauhawar kuɗin ruwa, biyan bashi mai nauyi da kuma tsauraran sharuɗan karɓar bashi.

Idan ba a magance waɗannan matsalolin kuɗin ba, burin da Tarayyar Afrika ke da shi na samun adalci da daidaito ba zai cika ba.

Babban taron baya bayan nan na Tarayyar Afrika, bisa taken "Adalci Ga Ƴan Afrika da Masu Nasaba da Afrika ta Hanyar Biyan Diyya" ya bayyana buƙatar gaggawa da ake da ita, ta yin adalci kan rashin adalcin da aka tafka a tarihi.

Sai dai, tattaunawa kan biyan diyya dole a aiwatar da shi tare da bincike mai zurfi kan ƴancin cin gashin kai na tattalin arziki da kuma nuna bambanci ba ƙaƙƙautawa da ke kawo wa cigaban Afrika tsaiko.

Tabbatacciyar Hanyar Samar da Kuɗaɗe:  Ginshiƙin fafutikar da Tarayyar Afrika ke yi wajen neman adalci da daidaito.

Tsare tsaren tattalin arzikin da ya dawwamar da rashin dogaro da kai da Afrika ba ta yi kan kuɗi, su ma wasu nau'ikan rashin adalci ne, da ke buƙatar kulawa kamar irin wacce aka bai wa kurakuren da aka tafka bisa tarihi da Babban Taron Tarayyar Afrika na 2025 zai tattauna a kai.

Tabbatacciyar Hanyar Samar da Kuɗaɗe:  Ginshiƙin fafutikar da Tarayyar Afrika ke yi wajen neman adalci da daidaito.

Wani sabon mataki kan tabbatacciyar hanyar samar da kuɗaɗe da ta fi mayar da hankali kan yafe bashi, ƴancin cin gashin kai na tattalin arziki da kuma zuba jari yana da mahimmanci wajen kai wa ga cim ma burin Tarayyar Afrika na wanzar da adalci da daidaito.

Tsare tsaren tattalin arzikin da ya dawwamar da rashin dogaro da kai da Afrika ba ta yi kan kuɗi, su ma wasu nau'ikan rashin adalci ne, da ke buƙatar kulawa kamar irin wacce aka bai wa kurakuren da aka tafka bisa tarihi da babban taron ke son magancewa.

Matsalar tattalin arziki da hauhawar kuɗin ruwa ke haifarwa

Afirika ita ce nahiyar da ta fi kowacce karɓar bashi daga waje da ya fi ƙarfin illahirin samunta.

Taƙaitacciyar hanyar hada-hadar kuɗaɗe ɗaya ce daga cikin tasirin nan-take na hauhawar kuɗin ruwa, saboda gwamnati na amfani da kaso mafi tsoka na kuɗaɗen shigarta wajen biyan bashi, tana barin ɗan sarari kaɗan wa harkokin zuba jari da za su kawo cigaba.

Wani rahoton baya bayan nan da Gidauniyar Mi Ibrahim ta fitar ya nuna cewa ƙasashen Afrika guda 25 sun fi kashe kuɗaɗe kan biyan bashin da suka karɓo daga waje fiye da a kan kiwon lafiya tsakanin 2019 zuwa 2021.

Sauya akalar kuɗaɗen shi ke haddasa rashin samun isassun kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya ƙasa, musamman ilimi, kiwon lafiya da jin daɗin jama'a-manyan ɓangarorin magance talauci da nuna bambanci.

 Bugu da ƙari, hauhawar kuɗin ruwa na taimakawa bashi ya taru ya yi yawa. Galibin ƙasashen Afrika ba su da maki mai yawa a ma'aunin karɓar bashi, abin da yake haddasa hauhawar kuɗin ruwansu da kuma ta'azzara harkar zuba jari.

Yanayin a yawancin lokaci yana sa wa bashi ya yi wa ƙasa katutu, inda ƙasashe ka kokawar biyan basussukan da ake bin su ba tare da sun ƙara cin wani bashin ba.

A cewa Bankin Duniya, fiye da rabin ƙasashen masu ƙaramin ƙarfi a Afrika, a halin yanzu, wataƙila bashi ya yi musu katutu ko kuma suna fuskantar bashi mai nauyin gaske - yanayin da matsin tattalin arzikin duniya da kuma shugabanci mai rauni suka ta'azzara.

Tasirin bashi kan zamantakewa da harkokin raya ƙasa a bayyane suke. Sauya akalar kuɗaɗe ga biyan bashi na taƙaita zuba jari a fannonin bunƙasa masu dogon zango, da katse bunƙasar tattalin arziki da kuma ta'azzara matsalolin zamantakewa.

Hakan illa ce musamman a nahiyar da matsayin talauci yana sama kuma a inda mafi yawa daga al'umma sun dogara ne kan hidimar hukumomin gwamnati domin samun biyan buƙatunsu na yau da kullum.

 Sharuɗa masu tsauri da kuma dimokuraɗiyya 'mara zaɓi'

Hukumomin kuɗi na duniya kamar Hukumar Bayar da Lamuni ta duniya ( IMF) da kuma Bankin Duniya a galibin lokaci suna ƙaƙaba sauye sauye masu nasaba da kasuwa ta yi halinta a matsayin sharuɗan bayar da tallafi ga ƙasashe masu tasowa har da Afrika.

Waɗannan sauye sauyen galibi sun haɗa da matakan tsuke bakin aljihu, da miƙa cibiyoyin walwalar jama'a ga ƴan kasuwa da kuma manufofin janye tallafi a matsayin sharuɗa kafin a bayar da tallafin kuɗi.

An yi suka sosai kan manufofin a ƙyale kasuwa ta yi halinta saboda mummunan tasirinta kan zamantakewa, da suka haɗa da ƙaruwar talauci, rasa ayyukan yi da kuma hukumomin gwamnati masu rauni.

 Bincike ya alaƙanta agendar masu aƙidar a ƙyale kasuwa ta yi halinta da koma-bayan cin gajiyar dimokuraɗiyya a Afrika, saboda ƴan ƙasa da yawa suna ganin an katange su daga sharɓar romon dimokuraɗiyya.

Masanin tattalin arziki kan cigaba Thandika Mkandawira ya kwatanta wannan lamari yadda ya kamata da cewa "dimokuradiyya mara zaɓi", inda ake tilastawa gwamnatocin ƙasashen Afrika da ke neman tallafin kuɗi, su miƙa wuya ga cibiyoyin kuɗi na waje, abin da ke bai wa al'umma ƙaramin zaɓin tattalin arziki.

A irin wannan yanayin, matakan dimokuraɗiyyar na zama holoƙo, domin mutanen da ba a zaɓa ba ne ke yanke shawara kan manyan matakan tattalin arziki da ake ɗauka a maimakon gwamnatocin da ƴan ƙasa suka zaɓa. Hakan ba yana kawo nakasu kan halaccin gwamnati a idon ƴan ƙasa ne ba kaɗai, har wa yau yana ƙara ta'azzara nuna bambanci.

Kafin haƙa ta cim ma ruwa a neman adalci da daidaito da AU take yi, wajibi ne a saka batun tabbatacciyar hanyar samar da kuɗaɗe a gaba gaban ajandar.

 Nuna bambanci na tattalin arziki,ko shakka babu, yana haddasa mummunan rashin adalci da ke ƙara dawwamar da nuna bambanci nan dai da AU ke son kawarwa.

Matakin neman adalci mai fuska biyu

Idan shugabannin Afrika za su yi nasara wajen tabbatar da an yi adalci ta hanyar bayar da diyya, dole su yi amfani da mataki mai fuska biyu - ɗaya da ke magance rashin adalcin da aka tafka a baya yayin da kuma a lokaci guda suna tunkarar rashin adalcin tattalin arziki da ake yi a halin yanzu.

Biyan diyya sakamakon ba daidai ba da aka yi a baya zai kawo ƙaramin tasiri ne muddin ƙasashen Afrika suka ci gaba da kasancewa cikin ƙangin bashi da kuma rashin dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki.

Muhimmancin abu a wannan matakin shi ne buƙata da ke akwai ta samar da sabuwar dabarar tabbatacciyar hanyar samar da kuɗi da ta muhimmantar da ƴancin cin gashi kai na tattalin arziki da kuma rage raunin da nahiyar ke da shi wajen tunkarar lamaran da za su iya shammacin ta daga waje.

Wannan matakin dole ya ƙunshi sharuɗan bayar da bashi masu  sauƙi sosai, da matakan yafe bashi, da kuma samun bashi mai sauƙin biya.

Wajibi ne su ma ƙasashen Afrika su duba dabarun sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗe, kamar asusun raya yanki da zuba jarin ƴan ƙasa mazauna ƙasashen duniya, domin raba ƙafa kan hanyoyin shigar kuɗaɗensu, da kuma rage yawan dogaro da masu bayar da bashi na waje.

Bugu da ƙari, dole ne gwamnatocin ƙasashen Afrika su mahimmantar da nemo wasu hanyoyin samun kuɗin shiga kamar karɓar haraji, da ɗaukar matakan yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma gwamnatin ta san da zaman sana'o'in da a baya ba a yin lissafi da su.

Ƙarfafa yadda ake tafiyar da cibiyoyin kuɗi na gwamnati da kuma kyautata gaskiya a matakan karɓar bashi shi ma zai zama mai muhimmanci wajen tabbatarwa an yi amfani da kuɗaɗen da aka ciwo bashi wajen ayyukan cigaba a maimakon a yi asarar su ta hanyar cin hanci da rashawa ko almubazzaranci.

Wata sabuwar dabarar tunkarar tabbatacciyar hanyar samar da kuɗi-wacce ta muhimmantar da yafe bashi, ƴancin cin gashin kan tattalin arziki da kuma hidima wa al'umma-zai zama muhimmi wajen cicciɓa burin AU na neman adalci da daidaito.

 idan ba a kawar da matsalolin kuɗi da ke kawo tarnaƙi ga cigaban nahiyar ba, alƙawarin da aka ɗauka na samun adalci zai ci da zama mafarki kuma nuna bambanci zai ci gaba da wanzuwa.

 Wajibi ne gwagwarmayar neman diyya ta tafi kafaɗa da kafaɗa da fafutikar samun ƴancin tattalin arziki-wanda ya sanya buƙatu da burace buracen ƴaƴan Afrika a gaba gaba cikin ajandar cigaban nahiyar.

Mubarak Aliyu mai sharhi kan harkokin siyasa ne kuma marubuci da ke rubutu kan Afrika ta Yamma da kuma yankin Sahel. Abubuwan da ya fi sha'awar rubutu a kai sun haɗa da shugabanci da kuma cigaba da ya shafi kowa da kowa.

Togaciya: Ra'ayin da wannan marubucin ya bayyana bai zama dole ya zo daidai da ra'ayi, hange da manufofin TRT Afrika ba.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us