Kamar yadda yake a addinance, daga ranar 8 ga watan Zul Hijjah ne alhazai ke fita Mina ƙwansu da ƙwarƙwata don fara ibadar Aikin Hajji a duk shekara.
Daga wannan rana, birnin Makkah kan rore ya zama sai ainihin mazauna cikinsa ne kawai za su saura, su ɗin ma sai wadanda ba sa Aikin Hajji a wannan shekara.
A irin wannan rana ta 8 ga wata da ma 9 ga wata wato Ranar Arfa, Masallacin Harami ma yakan zama sai mutane kaɗan, har sai zuwa Ranar Sallah kuma wato 10 a lokacin da alhazai za su shiga don yin Ɗawafin Hajji.
Wataƙila ku dinga ayyana to me ke faruwa a waɗannan ranaku biyun da babu alhazai? Musamman ganin yadda hukumomin Saudiyya suka tsaurara a shekarun nan ta hanyar hana kowa shiga Makka sai mai izinin Aikin Hajji, ko da kuwa mazauna sauran garuruwan ƙasar ne.
A bana dai Saudiyya ta hana kimanin mutum 269,000 da ba su da izinin yin aikin hajji shiga birnin Makka inda mahukunta suka ce yawan jama’a da ake samu na nasaba da yawan waɗanda ba su da izinin yin aikin hajji da suke shiga birnin.
Abin da yake faruwa shi ne mafi yawanmutanen garin Makkah musamman mata da yara kan fita su je su wuni a Harami suna ɗawafi, har ma da maza da tsofaffi waɗanda ba su je Aikin Hajji ba.
Wani saƙo da aka wallafa shafin Facebook da ke kula da al’aumran Masallatai Biyu Masu Daraja na Inside Haramain ya ce “Yayin da miliyoyin mahajjata daga Makkah suka nufi Dutsen Arfa ranar 9 ga watan Zul Hijjah, mata cikin shigar baƙaƙen kaya da yara za su nufi Masallacin Harami domin gabatar da ɗawafi a Ka’bah, saboda kar harami ya kasance babu kowa.”
A wata al’ada ta mutanen Makkah ana kiran ranar da "Yawm Al-Kholeef” wadda ta samo asali daga kalmar Larabci mai suna “fanko.”
Sannan a ranar 9 ga watan Zul Hijjan ne kuma ake sauya rigar Ɗakin Kaaba (Mataaf).