GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Trump ya ba da shawarar yin watsi da tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi wa Netanyahu
Shugaban Amurka ya bayyana shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Firaministan Isra’ila a matsayin "bi-ta-da-ƙulli", yana mai kira ga hukumomi su soke shari’ar ko kuma su yi wa Netanyahu afuwa.
Trump ya ba da shawarar yin watsi da tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi wa Netanyahu
FILE PHOTO: U.S. President Trump meets Israeli PM Netanyahu in Washington / Reuters
26 Yuni 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a yi watsi da shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Firaym Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ko kuma a yi masa afuwa, yana mai bayyana shari’ar a matsayin "bi-ta-da-ƙulli."

"Ya kamata a soke shari’ar Netanyahu nan-take ko kuma a yi wa babban jarumin afuwa," kamar yadda Trump ya wallafa shafinsa na Truth Social ranar Laraba.

Ya bayyana Netanyahu a matsayin "Babban Firaminista na lokacin yaƙi" na Isra’ila, yana mai cewa ya yi mamakin jin cewa ana tsammanin Netanyahu a kotu ranar Litinin, duk da cewa ƙasar na fuskantar tashin hankali da Iran.

"Na gigice da na ji cewa Isra’ila, wadda kwanan nan ta ga lokacinta mafi daraja, ta ci gaba da wannan yaƙin ban dariyar kan Firamnistansa," in ji Trump.

"Babu wanda na sani wanda zai iya aiki sosai da wani shugaban Amurka fiye da Netanyahu."

Trump ya ƙara da duk da cewa Amuka ta "ceci" Isra’ila a lokacin rikici na baya bayan nan da Iran, "yanzu lokaci ne da Isra’ila za ta ceci Netanyahu."

Ya bayyana Netanyahu a matsayin shugaban Isra’ila da ya fi jarumta da ƙwarewa.

Cin hanci da zamba da cin amana

Kalaman Trump sun nuna wani sauyi da ya bayyana na ingancin alaƙa tsakanin mutanen biyu, bayan rahotannin saɓanin da ke tsakaninsu a kwanan baya.

Rashin jituwarsu a baya dai ta samo asali ne daga wasu batutuwa, ciki har da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza da kuma alaƙa da Iran kafin tashin hankali na kwana kwanan nan.

Masharhanta sun ce rashin jituwar ta sake fitowa fili a lokacin da Trump ya je rangadi a Gabas Ta Tsakiya kwanan nan, inda ya mayar da Isra’ila saniyar-ware — a karon farko da wani shugaban Amurka ya yi hakan.

Cikin kwanakin da aka yi kafin a yi ziyarar, Trump ya yi yarjejeniyar tsagaita wuta da ‘yan Houthi a Yemen ba tare da neman su daina kai hare-hare kan wurare a Isra’ila ba. 

Ya kuma amince da fara tattaunawa kai-tsaye da Hamas, a lokacin da rahotanni suka ce tawagarsa ta ba da damar samar da yadda za a shigar da kayayyakin agaji cikin Gaza idan aka sako wani ɗan Amurka kuma ɗan Isra’ila.

Shari’ar Netanyahu — kan tuhume-tuhumen cin hanci da zamba da kuma cin amana — an fara ta ne tun shekarar 2020.

An dakatar da shari’ar sau da yawa tun wancan lokacin, inda Netanyahu yake sawa a ɗage ta saboda kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma rikicin Lebanon.

A shari’a ta farko, an tuhumi Netanyahu da matarsa, Sara, da laifin karɓar kayan alfarma irin su sigari da kayan ado da giya da darajarsu ta kai dala 260,000 daga attajirai da ‘yan siyasa.

Sauran ƙararrakin suna tuhumar cewa Netanyahu ya yi yunƙurin cim ma yarjejeniya domin kafafen watsa labaran Isra’ila biyu su riƙa yin labarai masu daɗi a game da shi.

Ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.

Amurka na da hannu a ciki

Netanyahu yana kuma fuskantar tuhume-tuhumen laifukan yaƙi da take haƙƙin bil’Adama, inda kotun hukunta manyan laifuka ta ba da sammacin kamo shi da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant a watan Nuwamban shekarar 2024 saboda zalunci a Gaza, inda Falasɗinawa suka tabbatar da cewa an kashe mutum 56,000, yawancinsu mata da ƙananan yara.

Ana fargabar cewa kimanin Falasɗinawa 11,000 ɓaraguzan gine-ginen da aka lalata  suka binne, in ji kamfanin dillancin labaran gwamnati na Falasɗinawa WAFA.

Sai dai kuma masana suna ganin cewa adadin waɗanda aka kashe ya zarce abin da hukumomin Gaza suka sanar, suna masu kiyasta cewa zai kai kimanin 200,000.

Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Washington tana ware dala biliyan  3.8 a ko wace shekara ga ƙawarta ta tsawon lokaci.

Tun watan Oktoban shekarar 2023, Amurka ta kashe sama da dala biliyan 22 kan tallafa wa kisan kiyashin Isra’ila a Gaza da kuma yaƙi da ƙasashe masu maƙwabtaka. Duk da cewa manyan jami’an Amurka suna sukar Isra’ila  game da yawan mace-macen fararen-hula a Gaza, kawo yanzu Washington ta ƙi amincewa da kiraye-kirayen da ke neman ta gindaya sharruɗa kan ba da makamai [ga Isra’ila].

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us