Kamfanin haƙar ma’adanai na Sibanye Stillwater ya ca ana ƙoƙarin ceto mutane 289 da suka maƙale a wajen haƙar ma’adanan zinare na kamfanin da ke Kloof kusa da birnin Johnnesburg.
“Muna tabbatar da cewa an samu haɗari a Kloof 7, kuma mun duƙufa wajen ƙoƙarin samar musu da hanyar fitowa, inda daga nan kuma za mu fito da ma’aikatan,” kamar yadda kakakin kamfanin na Sibanye ya bayyana a ranar Juma’a.
Kakakin ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci.
“Muna fatan cewa za a warware matsalar zuwa tsakiyar ranar yau,” a cewar kakakin.
Tun da farko, Ƙungiyar Masu Haƙar Ma’adanai ta ƙasar (NUM) ta ce ta samu rahotannin hatsarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe goma na dare a ranar Alhamis.