GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Netayahu ya tabbatar da cewa Isra'ila na taimaka wa gungun masu makamai da ke adawa da Hamas a Gaza
Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da cewa Israila tallafa wa wata kungiyar masu ɗauke da makamai da ke adawa da Hamas, da ke karkashin Yasser Abu Shabab, a lokacin da ake zargin cewa kungiyar na yi aikata laifuka a madadin Isra'ila.
Netayahu ya tabbatar da cewa Isra'ila na taimaka wa gungun masu makamai da ke adawa da Hamas a Gaza
"Ia baik, menyelamatkan nyawa askar Israel." - Netanyahu / Reuters
7 Yuni 2025

Firaminista Benjamin Netanyahu ya amince cewa Isra'ila na goyon bayan wata kungiya mai ɗauke da makamai a Gaza da ke adawa da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, bayan kalaman da wani tsohon minista ya yi na cewa Isra'ila ta miƙa mata makamai.

Kafofin yaɗa labaran Isra'ila da na Falasdinu sun ruwaito cewa ƙungiyar da Isra'ila ke aiki da ita wani ɓangare ne na ƙabilar Bedouin ƙarƙashin jagorancin Yasser Abu Shabab.

Hukumar kula da Hulda da Ƙasashen waje ta Tarayyar Turai (EFCR) ta bayyana Abu Shabab a matsayin shugaban ƙungiyar masu aikata laifuka a yankin Rafah da ake zargi da wawure manyan motocin agaji.

Memba na Majalisar Isara’ila Knesset kuma tsohon ministan tsaro Avigdor Liberman ya shaida wa kafar yada labarai ta Kan cewa gwamnati, bisa umarnin Netanyahu, "tana ba da makamai ga gungun masu laifi da saura masu aikata laifuka".

"Mene ne fallasar Liberman? Majiyoyin tsaro sun kafa wata ƙabila a Gaza da ke adawa da Hamas? Menene laifin hakan?" a cewar Netanyahu a wani faifan bidiyo da aka saka a shafukan sada zumunta ranar Alhamis.

"Hakan yana da kyau, yana ceto rayukan sojojin Isra'ila."

Michael Milshtein ƙwararre kan harkokin Falasdinu a cibiyar Moshe Dayan da ke birnin Tel Aviv ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ƙabilar Abu Shabab wani ɓangare ne na kabilar Bedouin da ke kan iyakar Gaza da yankin Sinai na Masar.

Wasu daga cikin ‘ya’yan ƙabilar, in ji shi, suna da hannu a “dukkan ayyukan muggan laifuka, da safarar miyagun kwayoyi, da makamantansu”.

'Gungu'

Milshtein ya ce Abu Shabab ya shafe lokaci a gidan yari a Gaza kuma a kwanakin baya manya a danginsa sun yi Allah wadai da shi a matsayin "mai haɗin gwiwa kuma dan daba".

"Da alama a zahiri Shabak (Hukumar Tsaro ta Isra'ila) ko kuma (sojoji) sun yi tunanin cewa abu ne mai kyau mayar da wannan ƙungiya ta gungun ‘yan ta’adda, zuwa wakili, don ba su makamai da kuɗi da mafaka" daga ayyukan sojojin, in ji Milshtein.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar Hamas ta kashe ‘yan ƙungiyar hudu kwanaki da suka wuce.

Hukumar ta ECFR ta ce an bayar da rahoton cewa Hamas ta daure Abu Shabab a baya bisa laifin safarar miyagun kwayoyi. An ce Hamas ce ta kashe ɗan’uwansa a wani farmaki da ƙungiyar ta kai kan ayarin motocin MDD.

Isra'ila tana yawan zargin Hamas da ta kwashe kusan watanni 20 tana yaƙi da ita, da wasoso kan ayarin motocin agaji a Gaza.

Hamas ta ce ƙungiyar ta zabi cin amana da sata a matsayin hanyarsu, ta kuma yi kira ga fararen hula da su yi adawa da su.

Hamas da ke mulkin Gaza kusan shekaru 20, ta ce tana da shaidun “ƙarara kan yadda ake haɗaka tsakanin Isra’ila da wadannan gungun ‘yan fashi da makami, da kuma su kansu sojojin makiya, wajen wawure kayayyakin agaji da kuma kirkirar matsalar jin ƙai da ke ƙara ta’azzara wahalhalun da Palasdinawa ke fuskanta.

The Popular Forces, kamar yadda kungiyar Abu Shabab ta kira kanta, ta faɗa a shafin Facebook cewa "ba ta taba zama, kuma ba za ta taba zama ‘yar koren mamaya ba".

Ya kara da cewa "Makamanmu masu sauki ne, wadanda suka tsufa, kuma sun zo ne ta hanyar tallafin mutanenmu."

Milshtein ya kira matakin da Isra'ila ta dauka na bai wa wata ƙungiya irin su Abu Shabab makamai a matsayin "rashin tunani, ba wani abu da za ka iya kwatanta shi da dabara ba".

"Ina fatan lamarin ba zai ɓuge da zamma wani babban bala'i ba," in ji shi.

A watan Nuwamban da ya gabata ne Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta bayar da sammacin kame Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.

Har ila yau Isra'ila na fuskantar shari'ar kisan kiyashi a kotun duniya kan laifukan yaki da ta aikata kan fararen hula a yankin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us