AFIRKA
2 minti karatu
An saka tsohon ministan kuɗin Ghana cikin waɗanda Interpol ke nema ruwa-a-jallo
An zargi Ken Ofori-Atta da kaucewa gurfanarwa a kotu, da amfani da office don amfanin kan sa
An saka tsohon ministan kuɗin Ghana cikin waɗanda Interpol ke nema ruwa-a-jallo
Ofori-Atta shi ne tsohon ministan kudi a zamanin mulkin Nana Akufo-Addo tun daga 2017 zuwa 2024 / Getty Images
7 Yuni 2025

Rundunar ‘Yan sanda ta ƙasa da ƙasa Interpol ta saka tsohon ministan kuɗin Ghana Ken Ofori-Atta cikin waɗanda take nema ruwa-a-jallo a ranar Juma’a saboda kauce wa gurfanarwa, kamar yadda wata sanarwa ta Ofishin Mai Shigar da Ƙara na Musamman na Ghana ta bayyana.

Ofori-Atta, wanda a baya aka bayar da sammacin kama shi bisa zargin yin amfani da ofishin gwamnati don amfanin kansa, bai koma gida ba kuma yana ci gaba da zama a ƙasashen waje.

Interpol ta sake shi cikin waɗanda ake nema ruwa a jallo, saboda ya ƙi bayyana a gaban shari’a.

Ko da yake sanarwar ba ta kai ga sammacin kama mutum kai tsaye daga hukumar da ke kula da harkokin shari'a a ƙasar ba, tana zama matsayin buƙatar a tsare mutumin domin mika shi ga ƙasar da take nemansa.

Sanarwar ta kuma yi zargin cewa tsohon ministan mai shekaru 65 ya haddasa gagarumar asarar kudi ga ƙasar a lokacin da yake riƙe da muƙami.

Ofori-Atta ya kasance ministan kuɗin Ghana daga watan Janairu na 2017 zuwa Fabrairu 2024, a lokacin mulkin New Patriotic Party (NPP).

A watan Janairu, Shugaba John Dramani Mahama, wanda ya karɓi mulki kwanan nan, ya ƙaddamar da wani kwamitin ayyuka na musamman don ƙwato dukiyar ƙasa, mai suna Operation Recover All Assets, da nufin yaƙi da cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati da kuma kashe dukiyar kasa ta hanyar da bai kamata ba.

Ya zuwa yanzu, rundunar ta karɓi rahotannin cin hanci da rashawa da suka shafi sama da dalar Amurka biliyan 20.

Sai dai, Mahama na fuskantar sukar jam bainar jama'a saboda janye kararraki da ake yi wa wasu tsoffin abokansa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us