Rundunar sojan Amurka ta ɗauke wasu jiragenta na sama da na ruwa daga wasu sansanoni da Iran za ta iya kai wa hari cikin sauƙi a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda jami’an Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ranar Laraba.
Matakan na zuwa ne yayin da Shugaba Donald Trump ya sa duniya take jiran ko Amurka za ta fara taimakawa wajen kai hare-hare kan tashoshin nukiliyar Iran da kuma tashoshin makamai masu linzaminta yayin da mutane suka tserewa daga baban birnin ƙasar a rana ta shida da fara hare-hare ta sama.
A wani ɓangaren kuma, ofishin jakadancin Amurka a Qatar ya bada sanarwa ranar Alhamis cewa zai taƙaita iya yadda jami’anta za su iya shiga sansanin sojin sama na Al Udeid, sansanin sojin Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya, wanda ke cikin hamada a waje birnin Doha.
Ofishin jakadancin ya shaida wa jami’ai da kuma ‘yan ƙasar Amurka su mayar da hankali sosai “wajen yin taka-tsantsan game da rikicin da ke faruwa a yankin ".
Jami’an biyu, waɗanda suka yi magana bisa sharaɗin sakaya sunayensu, sun ce sauya wa jiragen sama da na ruwa wuri wani ɓangare ne na kare dakarun Amurka, amma sun ƙi su bayyana jirage nawa aka sauya wa wurare ko kuma inda aka kai su.
Ɗaya daga cikin jami’an ya ce an ɗauke jiragen da ba sa cikin wuri mai ƙarfi daga sansanin sojin Al Udeid kuma an ɗauke jiragen sojin ruwa daga tashar jiragen Ruwa ta Bahrain inda ayarin jiragen ruwan sojin na biyar yake.
"Ba wani abin da ba a saba gani ba ne," in ji jami’in. "Kare dakaru shi ne abin da aka fi bai wa muhimmanci."
An kai kayayyakin yaƙin ruwan Amurka zuwa Gabas Ta Tsakiya
Reuters ta ba da rahoto a wannan makon game da tafiyar jirgin da ke kara wa jiragen sama mai zuwa Turai da kuma sauran kayayyakin yaƙi zuwa Gabas Ta Tsakiya, ciki har da ƙarin jiragen yaƙi.
Wani jirgin ruwa mai dakon jiragen sama na yaƙi na kan hanyarsa zuwa Gabas Ta Tsakiya.
Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi ta sama ranar Juma’a bayan ta ce ta yi imanin cewa Iran ta kusa samar da makamin nukiliya.
Iran ta musanta kera makaman nukiliya.
Iran ta sanar da Washington cewa za ta mayar da martani da ƙarfi ga Amurka idan ta shiga yaƙin Ira’ila kai-tsaye, kamar yadda Jakadan Iran a Majalisa Ɗinkin Duniya ya bayyana a birnin Geneva ranar Laraba.