AFIRKA
2 minti karatu
Shugaba Tiani na Nijar ya ce har yanzu Faransa ba ta daina yi musu bi-ta-da-ƙulli ba
Shugaban Tiani ya zargi Faransa da hannu a kusan duka rikice-rikicen da suka faru a ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Pakistan da Afghanistan da Iraƙi da Syria da Libiya.
Shugaba Tiani na Nijar ya ce har yanzu Faransa ba ta daina yi musu bi-ta-da-ƙulli ba
Ya bayyana cewa Faransa da ƙawayenta na amfani da rikicin da suke haddasawa a ƙasashe marasa ƙarfi domin samun damar kwasar arziƙinsu. / RTN
1 Yuni 2025

Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana cewa har yanzu ƙasar Faransa ba ta daina bin su da sharri ba inda ya zarge ta da yi wa Nijar maƙarƙashiya iri daban-daban tun bayan hawan su mulki.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata hira ta talabijin ta kai tsaye da ya yi da gidan talabijin na Nijar RTN a ranar Asabar.

Shugaba Tiani ya zargi Faransa da hannu a kusan duka rikice-rikicen da suka faru a ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Pakistan da Afghanistan da Iraƙi da Syria da Libiya.

Ya bayyana cewa Faransa da ƙawayenta na amfani da rikicin da suke haddasawa a ƙasashe marasa ƙarfi domin samun damar kwasar arziƙinsu.

“Duk ƙasashen nan idan suna cikin tashin hankali, sai a samu a saci arziƙinsu yadda ake so, a yi wa ‘yan ƙasa wulaƙanci yadda ake so, a hana su kwanciyar hankali a cikin ƙasarsu, a hana su hanyar hijira su je wata ƙasa domin samun mafaka,” in ji Janar Tiani.

Tsara kai hare-hare kan Nijar

Janar Tiani ya jinjina wa sojojin Nijar bisa yadda suke jajircewa a kullum domin kare ƙasar daga maƙiya da hare-haren ta’addanci.

Ya yi zargin cewa hare-haren da ake ci gaba da kai wa Nijar duk shiri ne na Faransa.

“Hare-haren da ake kai mana, tsara su ake yi. Tsari ne da Faransa da masu mara mata baya suka shafe fiye da shekara guda suna yi,” in ji Tiani.

Tiani ya yi zargin cewa kwanaki biyu kacal bayan sun karɓi mulki Faransa ta shirya wani taro kan yadda za a wargaza gwamnatin mulkin sojan da ta karɓi mulki a ƙasar.

Janar Tiani ya kuma zargi Faransar da ƙoƙarin haddasa rikicin ƙabilanci a Nijar tsakanin ƙabilun Nijar inda ya bayar da misalin yadda Faransar ta haddasa irin wannan rikici a ƙasar Rwanda.

Sakamakon matsalar tsaro da ake fama da ita a Nijar wadda ke shafar manoma, Janar Tiani ɗin ya ce kamar yadda a shekarar bara jami’an tsaro suka bai wa manoma da makiya tsaro, a daminar bana ma za a ɗauki wannan mataki wanda a cewarsa hakan na taimakawa wurin wadatar abinci.

MAJIYA:RTN
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us