DUNIYA
3 minti karatu
Ina ne Alligator Alcatraz - cibiyar tsare baƙin haure da ke kewaye da kadoji da macizai a Amurka?
Donald Trump zai ziyarci wannan cibiya a yau.
Ina ne Alligator Alcatraz - cibiyar tsare baƙin haure da ke kewaye da kadoji da macizai a Amurka?
FILE PHOTO: US President Donald Trump is set to visit Alligator Alcatraz on Tuesday. / Reuters
1 Yuli 2025

Shugaban Amurka Donald Trump zai halarci taron buɗe cibiyar tsare 'yan gudun hijira da ake kira “Alligator Alcatraz” a ranar Talata, wadda aka gina a cikin jeji mai cike da macizai da kadoji a Florida.

Masu suka ga matakan Trump na tsauraran dokoki kan baƙin haure sun bayyana wannan shawara a matsayin rashin tausayi, yayin da masu kare muhalli suka nuna adawa da ginin cibiyar a cikin gandun daji na ƙasa.

Amma Fadar White House ta rungumi sunan da aka saka wa cibiyar, tana kwatanta ta da tsohon gidan yari na Alcatraz da ke tsibiri a San Francisco Bay, wanda Trump ke son sake buɗewa.

“Akwai hanya daya kawai zuwa ciki. Wurin yana keɓe kuma kewaye da dabbobi masu hatsari a yanayi mai sarƙaƙiya,” in ji Sakatariyar Yada Labarai Karoline Leavitt a ranar Litinin.

Da aka tambaye ta ko kada da macizai suna cikin “tsarin ginin,” Leavitt ta amsa: “Idan kana da masu laifi kamar masu kisan kai da masu fyaɗe a cibiyar tsarewa da ke kewaye da kada, e, ina ganin hakan zai hana su ƙoƙarin tserewa.”

Duk da cewa jami’an gwamnatin Trump suna yawan nuna cewa suna mayar da hankali kan masu laifi masu tsanani, yawancin baƙin haure marasa laifi sun fada cikin wannan kamun.

Ciyayi

Florida, jihar kudu maso gabashin da gwamnan jam’iyyar Republican mai ra’ayin mazan jiya Ron DeSantis ke jagoranta, ta sanar a makon da ya gabata cewa tana gina wannan wurin da ake ƙiyasta kudinsa ya kai dala miliyan 450.

Wurin yana wani wajen tsohon filin jirgin sama a tsakiyar jeji mai cike da bishiyoyi, da kuma wuraren da ake kira “cunkus da ciyayi” da ke cikin yankin kariya na Everglades.

Wurin shakatawa na kasa na Everglades ya shahara musamman a matsayin muhalli na kada, inda ake kiyasta cewa akwai kimanin kada 200,000. Kada na iya kaiwa tsawon kafa 15 idan sun girma sosai.

Kada da macizai

Ba a faye samun matsalolin da kada kan yi arangama da mutane ba a Florida. A duk fadin jihar, an samu rahoton da kada ya ciji mutane sau 453 daga tsakanin shekarar 1948 zuwa 2022, wanda 26 daga ciki suka yi sanadiyyar mutuwar mutane, a cewar Hukumar Kula da Dabbobin Daji ta Florida.

Amma hukumomi sun sake nanata hatsarin lamarin.

“Idan mutane sun fita, babu abin da ke jiran su sai kada da macizai,” in ji Babban Lauyan Florida James Uthmeier kwanan nan yayin da yake bayanin sansanin tsarewan.

Ya kuma bayyana wurin a matsayin “damar gina cibiyar tsarewa ta wucin gadi mai rahusa, saboda ba sai an kashe kudi sosai wajen gina katanga ba.”

Sakatariyar Yada Labarai ta White House Leavitt ta ce zai zama wurin da zai iya daukar mutum 5,000, amma hukumomin Florida sun ce zai dauki kimanin “bakin haure masu laifi” 1,000.

Gwamnatin Trump tana tallata “Alligator Alcatraz” yayin da take neman goyon baya don wani babban kasafin kudi da shugaban ke kokarin gabatarwa a Majalisar Dokoki a wannan mako.

“Babban Kyakkyawan Dokar Haraji” tana dauke da kudade don tsaurara matakan shige da fice na Trump, ciki har da karin wuraren tsare mutane.

“Na ƙagu lokacin buɗewar ya yi,” in ji Tom Homan, shugaban shige da fice na Trump, ga manema labarai a ranar Litinin yayin da aka tambaye shi game da ‘Alligator Alcatraz’.

Yunkurin korar bakin haure wani bangare ne na yakin neman tsaurara matakai kan shige da fice, ciki har da samamen da aka gudanar a Los Angeles wanda ya haifar da zanga-zanga kan Hukumar Kula da Shige da Fice da ta Kwastam (ICE).

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us