DUNIYA
2 minti karatu
Rasha ta yi iƙirarin ƙwace ƙauyuka biyu a yankunan Donetsk da Kharkiv na Ukraine
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa sojojin ƙasar sun ƙauce iko da ƙauyen Piddubne da kuma ƙauyen Sobolivka waɗanda ke yankunan Donetsk da Kharkiv na Ukraine
Rasha ta yi iƙirarin ƙwace ƙauyuka biyu a yankunan Donetsk da Kharkiv na Ukraine
A baya dai Rasha ta yi iƙirarin ƙwace garin Velyka Novosilka a ranar 27 ga Janairu / Reuters
6 Yuli 2025

Kasar Rasha ta ce sojojinta sun ƙwace wasu ƙauyuka biyu a yankunan Donetsk da Kharkiv na kasar Ukraine, a ci gaba da farmakin da take kaiwa a cikin ƙasar da rikici ya daɗe yana addaba.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa sojojin ƙasar sun ƙauce iko da ƙauyen Piddubne, wanda ke da nisan kimanin kilomita 22 da garin Velyka Novosilka, wani muhimmin yanki a gabashin Donetsk.

A baya dai Rasha ta yi iƙirarin ƙwace garin Velyka Novosilka a ranar 27 ga Janairu. Wannan gari yana kusa da inda yankunan Donetsk, Zaporizhzhia da Dnipropetrovsk suka haɗu.

Ƙauyen Piddubne na da nisan kilomita 20 daga magamar yankunan uku, haka kuma yana da nisan kilomita bakwai daga iyakokin Donetsk da Dnipropetrovsk.

Sanarwar ta kuma ce sojojin Rasha sun ƙwace kauyen Sobolivka, wanda ke da nisan kilomita da birnin Kupiansk, wanda ke ɗaya daga cikin fagagen dagan Moscow a arewa maso gabashin yankin Kharkiv.

Hukumomin Ukraine ba su fitar da wata sanarwa ba game da wannan iƙirari na Rasha, kuma ba a iya tabbatar da gaskiyar wannan batu ba saboda yaƙin da ake ci gaba da yi wanda a halin yanzu ya shiga shekararsa ta huɗu.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us