AFIRKA
2 minti karatu
Aƙalla mutum 11 sun mutu, da dama sun jikkata a zanga-zanga a Kenya
Hukumar kare hakkokin ɗan'adam ta ce rikici ya ɓarke a larduna 17 a yayin zanga-zangar Saba Saba domin nuna adawa da gwamnati, inda aka samu rahotannin tare motocin ɗaukar marasa lafiya da kama mutane.
Aƙalla mutum 11 sun mutu, da dama sun jikkata a zanga-zanga a Kenya
Tattakin Saba Saba na Jama'a a Nakuru / Reuters
8 Yuli 2025

Aƙalla mutane 11 ne suka mutu a yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a Kenya, in ji ‘yan sandan ƙasar ta Gabashin Afirka, inda sanarwar da suka fitar ta ƙara da cewa an jikkata ‘yan sanda dama.

Tun da fari, Hukumar Kare Hakkin Ɗan’Adam ta Ƙasa ta Kenya ta sanar da mutuwar mutane 10 a ranar Litinin, inda ta kuma ce mutane 29 sun jikkata.

Hukumar ta bayyana samun rahotannin yin garkuwa da mutane har sau biyu, an kama mutane 37 da kuma samun rahotannin sace-sace a larduna shida. A wani waje, waɗanda ake zargin ɓata-gari ne sun cinna wuta a ofishin Ofishin Cigaba na Mazaɓar Kerugoya.

An fara zanga-zangar ta Saba Saba a larduna 17 don tuna wa da zanga-zangar ranar 7 ga watan Yuli, da aka yi a ƙasar ta Kenya.

A yankin Kangemi na Nairobi, babban birnin ƙasar da garin Kitengela na gundumar Kajiado a ranar Litinin, kafafen yaɗa labarai na KTN da Citizen TV sun bayar da rahoton mutuwar mutane huɗu.

Masu bayar da agajin gaggawa sun bayyana gaza isa ga waɗanda lamarin ya rutsa da su sakamakon rufe hanyoyi da masu zanga-zangar suka yi, musamman a wasu yankunan Kangemi.

Ganau a Kangemi sun bayyana cewa an samu munanan arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, inda aka jiyo ƙarar harbe-harben bindiga.

An ci gaba da fuskantar rikici a gundumomin Kibra, Githurai da Mathsare da ke babban birnin Nairobi, inda masu zanga-zangar suka kunna wuta tare da rufe manyan hanyoyi.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us