GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Firaministan Isra'ila Netanyahu ya kamu da ciwon kumburin hanji
Netanyahu wanda a kwanakin baya aka yi wa tiyatar mafitsara sannan kuma aka saka masa na'ura a zuciyarsa domin taimaka wa bugun zuciyarsa, likitoci a halin yanzu sun gano yana fama da kumburin hanji.
Firaministan Isra'ila Netanyahu ya kamu da ciwon kumburin hanji
Netanyahu, wanda yake da shekara 75, ya kamu da rashin lafiya cikin dare, inda aka gano yana fama da kumburin hanji da rashin ruwa a jikinsa / Reuters
20 Yuli 2025

Likitoci sun gano Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, na fama da kumburin hanji wanda hakan zai sa ya huta na tsawon kwanaki uku, kamar yadda ofishinsa ya sanar a ranar Lahadi.

Netanyahu, wanda yake da shekara 75, ya kamu da rashin lafiya cikin dare, inda aka gano yana fama da kumburin hanji da rashin ruwa a jikinsa. A halin yanzu, yana karɓar magani ta hanyar yi masa ƙarin ruwa, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana.

Ofishinsa ya bayyana cewa yana samun lafiya kuma, "A karkashin jagorancin likitocinsa, firaminista zai huta a gida na tsawon kwanaki uku kuma zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati daga can."

An saka wa Netanyahu na’urar taimaka wa bugun zuciya a shekarar 2023, sannan a watan Disamba na bara, ya yi fama da ciwon mafitsara inda aka yi masa tiyata.

A cewar tashar Channel 12, firaministan ba zai halarci zaman majalisar Knesset na ranar Lahadi ba, kuma zaman shari'arsa a gaban Kotun Gundumar Tel Aviv an shirya shi a ranar Litinin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us