AFIRKA
2 minti karatu
Algeria ta bai wa jami’an ofishin jakadancin Faransa 12 wa’adin barin ƙasar
Faransa ta nemi Aljeriya ta dakatar da korar jami'an diflomasiyyarta 12 kuma ta yi barazanar ɗaukar mataki nan-take idan ba ta sauya umarnin ba.
Algeria ta bai wa jami’an ofishin jakadancin Faransa 12 wa’adin barin ƙasar
Dangantakar diflomasiyya ta taɓarɓare tsakanin Aljeriya da Faransa / AFP
14 Afrilu 2025

Aljeriya ta bai wa jami’an diflomasiyyar Faransa 12 sa’o’i 48 su bar ƙasar, kamar yadda ministan harkokin wajen Faransa ya bayyana ranar Litinin, yana mai ƙarawa da cewa wannan matakin na da alaƙa da kama ‘yan Aljeriya a Faransa.

"Ina kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da waɗannan matakan korar… idan wannan matakin na korar jam’ianmu bai sauya ba, ba mu da wani zaɓi face mu mayar da martani nan-take," in ji ministan harkokin wajen Jean-Noel Barrot.

Jami’an 12 sun haɗa da mambobin ma’aikatar cikin gida ta Faransa, kamar yadda wata majiya ta diflomasiyya ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP.

Ranar Juma’a, masu gabatar da ƙarar Faransa sun tuhumi ‘yan Aljeriya uku, ciki har da wani jami’in jakadanci kan zargin hannu a garkuwa da aka yi da wani shahararren ɗan Aljeriya, Amir Boukhors, a watan Afrilun shekarar 2024 a wata unguwa da ke wajen birnin Paris.

Tuhumar na zuwa ne a wani lokacin da ake zama ɗarɗar tsakanin Aljeriya da tsohuwar uwar gijiyarta, inda Algiers take iƙirarin cewa matakan na da zummar katse ƙoƙarin da ake na gyara dangantakar.

Boukhors, da aka fi sani  da suna "Amir DZ", wani mai adawa ne da gwamnatin Aljeriya wanda yake da fiye da mabiya miliyan ɗaya a TikTok.

Ya kasance a Faransa tun shekarar 2016 kuma an ba shi mafakar siyasa a shekarar 2023. An yi garkuwa da shi a watan Afrilun shekarar 2024 kuma an sake shi washe gari, in ji lauyansa.

Algiers na neman mutumin ya dawo ya fuskanci ƙuliya, bayan an ba da sammacin kamo shi, inda ake zarginsa da laifukan damfara da ta’addanci.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us