Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Nuh Yılmaz, ya bayyana mamayar da Isra'ila ta yi tsawon shekaru a matsayin babban cikas ga kafa ƙasar Falasdinu, yana mai kira ga al'ummar duniya su ɗauki matakan a-zo-a-gani da suka wuce na bayyana damuwa kawai don tabbatar da samun mafita ta kafa ƙasashe biyu.
“Abin da yake maimaituwa shi ne cewa ci gaba da mamayar ita ce babbar matsala a hanyar kafa ƙasar Falasdinu,” in ji Yılmaz a ranar Litinin yayin wani babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan mafita ta ƙasashe biyu, wanda aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York.
Yılmaz ya yi maraba da matakin da Faransa ta ɗauka na amincewa da ƙasar Falasdinu, yana mai cewa Ankara “na da kyakkyawan fatan cewa wasu ƙasashe da dama za su ɗauki irin wannan mataki nan ba da jimawa ba.”
Ya bayyana martanin da aka samu daga wakilan da kasashe mahalarta a matsayin wata alama ta damuwa ta duniya da kuma ƙwarin gwiwa na kawo ƙarshen wahalhalun da al'ummar Falasdinu ke fuskanta.
Ƙarfafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta
Ya ce, shawarwari da dama sun goyi bayan taimaka wa cibiyoyin Falasdinawa, tare da jaddada buƙatar ƙarfafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Ya ƙara da cewa kawo ƙarshen mamayar shi ne abin da ya fi ɗaukan hankali a tattaunawar, yana gargadin cewa shirye-shiryen Isra'ila na mamaye wasu yankuna, ciki har da kiran da majalisar dokokin Isra'ila ta yi kwanan nan, suna buƙatar martani cikin gaggawa daga ƙasashen duniya.
Yılmaz ya bayyana cewa wasu wakilai sun ba da shawarar kafa hanyoyin aiwatar da dokokin ƙasa da ƙasa da ka'idojin jin ƙai.
Ya kuma nuna cewa ana ƙara samun kira na sanya takunkumi kan Isra'ilawa ‘yan kama-wuri-zauna a yankunan da aka mamaye a Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus, tare da cewa Isra'ila kanta na iya fuskantar matakan tilasta wa saboda kasancewarta mai tallafa wa ayyukan mamaya ba bisa ka'ida ba.
‘Dakatar da Isra'ila daga korar Falasdinawa daga ƙasarsu’
Baya ga matsalar da ke ƙara ta'azzara a Gaza, Yılmaz ya ambato ci gaba da kwace filaye, da rushe gidaje, da kuma korar Falasdinawa daga yankunan da aka mamaye a Yammacin Kogin Jordan.
“Dole ne a dakatar da ayyukan Isra'ila na korar Falasdinawa daga ƙasarsu ba tare da wani jinkiri ba. Ba za mu iya tunanin kafa ƙasar Falasdinu ba tare da al'ummar Falasdinu ba,” in ji shi.
A duk tsawon lokacin da aka kwashe ana taron, wakilai sun jaddada gaggawar aiwatar da mafita ta kafa ƙasashe biyu, da amincewa da Falasdinu a matsayin cikakkiyar memba ta Majalisar Ɗinkin Duniya, da tabbatar da tallafin jin kai da sake gina Gaza, da dakatar da faɗaɗa matsugunan Yahudawa, da ƙarfafa haɗin gwiwar al'umma, da kuma tabbatar da tsaro da ɗa'a ta hanyar bin doka.
“Shawarwarin sun aika da saƙo mai ƙarfi: Dole ne al'ummar duniya ta yi aiki cikin gaggawa da ƙarfi don kare fatan samun mafita ta ƙasashe biyu, don tabbatar da ka'idojin doka da jin ƙai, da kuma zarta matakin bayyana damuwa zuwa aiwatar da hanyoyin ɗa'a,” in ji Yılmaz.