Wakilan Isra'ila sun tafi Qatar don tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza
Isra'ila za ta tura wata tawaga zuwa birnin Doha domin gudanar da wani sabon zagaye na tattaunawa kan tsawaita wa'adin tsagaita wuta a Gaza, bayan katse wutar lantarki a yankin Falasdinu.
Kashi na farko na tsagaita wuta ya kare ne a ranar 1 ga Maris ba tare da wata yarjejeniya kan matakan da za su biyo baya ba da za su iya tabbatar da kawo karshen yakin ba na dindindin.
Har ila yau Isra'ila ta dakatar da kai agajin da take kaiwa Gaza a daidai lokacin da ake tsaka mai wuya.
Hamas na zargin Netanyahu da yi wa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ƙafar-ungulu
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta zargi Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Gaza ta hanyar yunkurin bullo da taswirar da ta dace da manufofinsa na siyasa kan rayuwar mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su.
Netanyahu yana "kokarin kawo cikas ga yarjejeniyar, tare da sanya sabbin sharuddan da zai amfanar da kansa, tare da yin watsi da bukatun iyalan wadanda aka kama", in ji Izat al-Rishq, mamba a ofishin siyasa na Hamas, a cikin wata sanarwa.
Ya kara da cewa hanya daya tilo da za a bi ita ce kiyaye sharuddan yarjejeniyar da fara tattaunawa a mataki na biyu, yana mai gargadin cewa duk wani jinkirin da ake yi na bata lokaci ne da kuma yin amfani da makomar wadanda aka kama.
Wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai farmaki a masallacin Yammacin Kogin Jordan, inda suka far wa masu ibada
Wasu Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kai farmaki a wani masallaci da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan da ke arewacin kasar a lokacin da ake gudanar da sallar Ramadan a yammacin Lahadin da ta gabata, inda suka ci zarafin masu ibada tare da lalata abubuwan da ke cikin masallacin.
Thaer Haneni, wani mai fafutuka na yankin da ya halarci masallacin a yayin harin, ya ce harin ya shafi Masallacin Beit Sheikh da ke kauyen Khirbet Tana da ke gabashin garin Beit Furik.
Ya bayyana yadda wata motar soji mara lamba dauke da wasu mutane hudu da ke sanye da kakin sojin Isra'ila tare da wata karamar motar daukar kaya daga jami'an tsaro suka isa masallacin. Sai mutanen da suka sauka suka mamaye masallacin, ya ce.