AFIRKA
1 minti karatu
Gungun 'yan ta'adda a kan babura da motoci sun kashe sojojin Nijar 34
Maharan sun yi amfani da motoci takwas da babura sama da 200 wajen kai harin a Bani-bangou a ranar Alhamis.
Gungun 'yan ta'adda a kan babura da motoci sun kashe sojojin Nijar 34
Nijar na fama da yaki da 'yan ta'adda a ke da alaka da Alqa'eda da Daesh. / Getty
20 Yuni 2025

Ɗaruruwan ‘yan ta’adda ɗauke da makamai, da yawan su a kan babura, sun kai hari kan wani sansanin sojin Nijar da ke kusa da iyakar Mali, inda suka kashe aƙalla sojoji 34 da jikkata wasu 14.

Maharan - da ma’aikatar tsaro ta kira ‘yan ta’adda - sun yi amfani da motoci takwas da babura 200 wajen kai harin a sansanin da ke Bani-bangou, kamar yadda tashar talabijin din ƙasar ta sanar.

Ba ta bayyana wacce ƙungiyar ta’adda ce ta kai harin ba. Nijar, kamar sauran ƙasashen Sahel na Yammacin Afirka, na fama da ‘yan ta’adda da ke da alaƙa da Alqa’eda da Daesh.

Bayan kai harin, sojoji sun kai farmakai ta sama da ta ƙasa don amintar da yankin, in ji ma’aikatar ba tare da bayar da cikakken bayani ba game da harin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us