Rundunar tsaron ƙasa ta Nijar (GNN) ta kama ayarin masu yi wa ‘yan bindiga fataucin man fetur, inda cikin sa’o’i 48 ta ƙwace kimanin litar fetur 10,000 da ake ƙoƙarin kai wa masu tayar da ƙayar baya.
Rahotanni daga Nijar sun ce samamen da dakarun tsaron suka kai Tanout (a yankin Zinder) da Boutti da N'guiguimi (a yankin Diffa), sun bayyana alaƙar da ke tsakanin masu fasa-ƙauri da ƙungiyoyin ‘yan ta’dda.
Kafar watsa labarai ta Actu Nijar ta ruwaito cewa dakarun tsaron ƙasar sun samu bayanai da ke nuna cewa za a kai man fetur ga ‘yan Boko Haram da ke yankin Tafkin Chadi lamarin da ya sa dakarun suka kai samame kan mutanen da ke yi wa ‘yan ta’adda safarar man fetur tsakanin ranar 15 da 16 ga watan Yuni.
A ranar 16 ga watan Yuni, wata rundunar GNN ta musamman ta tare motocin a-kori-kura uku ƙirar Toyota Hilux a yankin N'guiguimi–Blabrim, a kan hanyarsu ta zuwa Tafkin Chadi.
A cikin motocin an samu mutum uku da jarkoki masu ɗaukar litar fetur 25 har guda 300 (lita 7,500 jumulla), da wayar salula ƙirar Thuraya da kuma wayoyi bakwai.
Kazalika a ranar 15 ga watan Yuni wasu ‘yan sintiri sun cafke wani ayari a ƙauyen Dalli, a ƙaramar hukumar Tanout. A nan ma an kama mutum uku, ciki har da wata mata a cikin wata mota ƙirar Nissan wadda ba a yi wa rajista ba. Kuma a cikin motar an samu man fetur da ya kai lita 2,075.
A ranar an sake wani kamu a Boutti inda aka samu jarkoki 85 wadda ko wace ke iya ɗaukar lita 25 na man fetur, lita 2,125 ke nan jumulla.
Ƙasar Nijar tana cikin ƙasashen da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a Yammacin Afirka.