Wani babban jami'in Kenya ya ce dole ne Iran da Isra'ila su bai wa ofisoshin diflomasiyya na ƙetare kariya bayan wani harin da aka kai a yankin Ramat Gan na Tel Aviv a ranar Alhamis, wanda tazarar wajen da aka kai harin ke da nisan mita dari da ofishin jakadancin kasar ta Kenya.
Babban sakatare a Ma'aikatar Harkokin Wajen Kenya Korir Sing'Oei ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, "bai kamata a keta ayyukan kasashen ketare a karkashin dokokin kasa da kasa ba, kuma dole ne a keɓe su tare da kare su daga haɗarin makamai a kowane lokaci."
Sing'Oei ya kuma bayyana sakon jakadan Kenya a Isra'ila, inda ya ce, ma'aikatan ofishin jakadancin suna aiki daga gida kuma suna cikin koshin lafiya.
A gefe guda kuma, Austria ta ce harin makamin mai linzami da aka kai a Ramat Gan bai shafi ofishin jakadancinta da ke Tel Aviv ba, kamar yadda mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana.
'Mitoci daga ofishin jakadanci'
Ofishin jakadancin Lithuania da ke Isra’ila bai samu matsala ba lokacin da makami mai linzami na Iran ya kai hari a unguwar Ramat Gan da ke Tel Aviv, in ji ma’aikatar harkokin wajen Lithuania a ranar Alhamis.
“Jakadan ya tabbatar da cewa ofishin jakadancin bai lalace ba, amma harin ya afka wa gine-gine masu nisan mita 200 daga ofishin jakadancin,” in ji kakakin ma’aikatar.
Makamai masu linzami na Iran sun kai hari kan manyan biranen kasar Isra'ila da suka hada da Tel Aviv, Ramat Gan, da Holon, da kuma asibitin Soroka da ke Beersheba, da ke kula da sojojin da ke yaki a yakin kisan kare dangi na Tel Aviv kan Falasdinawa a Gaza.
Iran ta mayar da martani ne bayan harin da Isra'ila ta kai a ranar 13 ga watan Yuni. Isra'ila ta kashe fiye da mutane 500 a Iran, a cewar jami'ai.