Fitaccen tauraron Bollywood, Saif Ali Khan, ya rasa ikon mallakar kadarorin kakanninsa da darajarsu ta kai biliyan 150 na kuɗin Indiya, Rupee.
Babbar Kotun jihar Madhya Pradesh a Indiya ta yanke hukunci cewa kadarorin sun shiga karkashin dokar 'Enemy Property Act,' wata doka da ta ayyana dukiyar da ta zama ta wasu da Indiya ke kallo abokan gaba tun a zamanin can baya a matsayin ta maƙiya, inda ta yi watsi da ƙarar da Khan da iyalinsa suka shigar, hukuncin da ya zama babban koma da kuma sanya takaici a zuƙata.
Alkali Sanjay Dwivedi, ya mayar da shari’ar zuwa kotun farko tare da ba da umarnin sake duba ƙarar da kammala shari’ar cikin shekara guda.
A wannan lokaci, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta News18 ta ruwaito, iyalin ba za su iya kiran kadarorin a matsayin nasu ba.
Khan yana da asali daga dangin sarauta da suka mulki tsofaffin masarautun Pataudi da Bhopal a Indiya.
Shekaru da dama, an san Khan da mahaifiyarsa da 'yan’uwansa mata a matsayin magadan halal na wannan gagarumar dukiya.
Khan da iyalinsa suna kuma fafutukar neman mallakar kadarorin mahaifinsa na iyalin Pataudi. Duk kadarorin sun shiga karkashin dokar 'enemy property' bisa dokokin Indiya.
Rigima kan kadarorin iyayen Saif Ali Khan ta fara ne a ranar 19 ga Disamban 2014, lokacin da mai kula da kadarorin ya fitar da sanarwa yana ikirarin cewa kadarorin iyalin Pataudi a Bhopal sun zama kadarorin 'enemy property.'
A ranar 25 ga Fabrairun 2015, an ayyana wadannan kadarorin a hukumance a matsayin kadarorin 'enemy property.' Daga baya, BAbbar Kotu ta jihar Madhya Pradesh ta bai wa iyalan damar ci gaba da amfani da kadarorin har zuwa lokacin da za a kammala shari’a.
Bayan yakin Indiya da China na 1962 da kuma yakin Indiya da Pakistan na 1965, Indiya ta gabatar da dokar Enemy Property Act, 1968, domin kula da kadarorin da ke cikin kasar da ke hannun 'yan kasar Pakistan.
Bisa wannan doka, gwamnatin Indiya tana da ikon ƙwace kadarorin da ke hannun mutanen da aka ayyana a matsayin 'abokan gaba,' wadanda suka koma China ko Pakistan yayin ko bayan 1947.
Wadannan kadarorin ana kula da su ne ta hannun wata hukuma mai suna Custodian of Enemy Property for India.
Pakistan ma tana da irin wannan doka mai suna Enemy Property Law, wadda aka kafa a 1969.
Gwamnatin Indiya ta kuma gabatar da wasu ƙa’idoji da dokoki, ciki har da Enemy Property Rules, 2015.
Umarnin da aka bayar daga 2018 zuwa 2020 sun bayyana hanyoyin da za a bi wajen canja, sayarwa, ko sarrafa kadarorin 'enemy property.'
Wadannan matakai suna tabbatar da tsari wajen sarrafa da kuma raba irin wadannan kadarori bisa tanadin dokar.
A 2017, an yi gyara ga dokar ta 1968 inda aka fadada ma’anar 'abokan gaba' don haɗa magadan su na doka da kuma masu gadon su, ko da kuwa suna da wata ƙasa daban.
A halin yanzu, hukuma tana rike da kadarori 13,252 na 'enemy property' da darajarsu ta kai sama da tiriliyan daya na Rupee na Indiya, ko kusan dala biliyan 11.5.
Matsalar iyalin Pataudi ba ta daban ba ce. Raja na Mahmudabad, Amir Mohammad Khan, ya fuskanci irin wannan rikici da ya dauki shekaru 32 kafin a warware.