AFIRKA
2 minti karatu
Somair: Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar mayar da kamfanin haƙar uranium na Faransa mallakinta
Kamfanin Orano na ƙasar Faransa ke da kaso 63 a kamfanin na Somair sai kuma gwamnatin Nijar ke da sauran kason, inda a halin yanzu gwamnatin ta Nijar ta sanar da ƙwace iko da gaba ɗaya kamfanin.
Somair: Gwamnatin Nijar ta yanke shawarar mayar da kamfanin haƙar uranium na Faransa mallakinta
Sanarwar ta bayyana wasu dalilai da suka haɗa da wa’adin yarjejeniyar hakar ma'adinan da ya zo ƙarshe a watan Disamba na shekarar 2023. / TRT Afrika Hausa
20 Yuni 2025

Gwamnatin Nijar a ranar Alhamis ta sanar da shirin mayar da kamfanin haɗin gwiwa na Somair na haƙar uranium zuwa mallakin Nijar ita kaɗai. Gwamnatin Nijar ɗin ce ta sanar sanar da wannan matakin wanda zai shafi kamfanin na Somair wanda kamfanin haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanin Orano na Faransa da Nijar.

Sanarwar ta bayyana wasu dalilai da suka haɗa da wa’adin yarjejeniyar hakar ma'adinan da ya zo ƙarshe a watan Disamba na shekarar 2023.

"Dangane da wannan ɗabi’a ta rashin sanin ya kamata da rashin bin doka da rashin adalci daga Orano, kamfani mallakar gwamnatin Faransa — ƙasa da ta nuna adawa fili ga Nijar tun ranar 26 ga Yuli, 2023 ... gwamnatin Nijar ta yanke shawarar, cikin cikakken ikon kanta, ta ƙwace mallakar Somair," in ji sanarwar.

Wannan matakin ya biyo bayan ƙara tsamin dangantaka tsakaningwamnatin Nijar da Faransar tun bayan juyin mulki da sojojin na Nijar suka yi a Yulin 2023.

Orano na da kaso 63% na hannun jari a Somair, yayin da kamfanin nan mallakar Nijar na Sopamin ke da kaso 37, amma duk da haka kamfanin na Faransa na a kulle tun bayan da gwamnatin sojin Nijar ta karɓi ikon hakar ma'adinan uranium ɗin.

Orano, wanda ke ta bin matakan sasanci da Nijar tare da shigar da ƙara a kotunan ƙasar kan matakan gwamnatin, ya yi ta gargaɗi kan tsoma bakin gwamnati a Somair, wanda ya ce yana kawo cikas ga ɓangaren kuɗin kamfanin.

A cewar wani rahoto daga Financial Times a watan Mayu, kamfanin ya kuma fara nazarin yiwuwar siyar da hannun jarinsa a wannan haɗin gwiwar ta hakar uranium.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us