DUNIYA
2 minti karatu
An kama 'yan Nijeriya da 'yan wasu ƙasashen kan zarginsu da zambar intanet a Pakistan
Hukumomin kasar sun kama wasu mutane 150 da ake zargi da yin zamba ta intanet, ciki har da baƙi 'yan ƙasashen waje 71.
An kama 'yan Nijeriya da 'yan wasu ƙasashen kan zarginsu da zambar intanet a Pakistan
Zamba ta intanet ta zama ruwan dare a duniya / Getty Images
9 Yuli 2025

Hukumomin da ke yaki da masu aikata laifuka a Pakistan sun ce sun kama wata kafar sadarwa ta kasa da kasa da ake zargi da aikata zamba ta intanet, inda suka kama mutane kusan 150 da ake zargi da aikata laifuka, ciki har da baƙi 71.

Hukumar binciken laifuka ta kasa (NCCIA) ta kai samame a wani gini da ke arewa maso gabashin Faisalabad, birni na uku mafi girma a kasar da kuma masana’antu, "bisa wani shiri" domin kama wadanda ake zargin, da suka hada da mata 18.

Mutanen da aka kaman sun hada da maza da mata 71 daga ƙasashen Philippines da Nijeriya da Bangladesh da Myanmar da Sri Lanka, da Zimbabwe.

Bayan haka, wata kotu a Faisalabad ta bayar da umarnin tsare duk wadanda ake tuhuma a gidan yari na NCCIA na tsawon kwanaki biyar.

A cewar NCCIA, wadanda ake zargin sun gudanar da wani shiri na Ponzi ne domin yaudarar jama’a da kuma tara makudan kudade ta hanyar sa hannun jari na bogi da kuma zamba ta zamani.

An shigar da jimillar kararraki bakwai da suka shafi zamba da kuma yaudara a kan wadanda ake tuhuma, wadanda suka kai hari ga wasu mutane da ba su ji ba, akasari ‘yan kasar Pakistan—ta hanyar yaudarar su cikin tsare-tsaren saka hannun jari na ƙarya ta intanet ta hanyar aika musu ta shafukan sakonnin sada zumunta.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us