Jirgin ruwan dakon mai dauke da tan 90,000 na man fetur zai bar matatar Dangote ta Nijeriya a karon farko zuwa nahiyar Asia, in ji wata majiya da ke da alaƙa da batun.
Tun bayan da matatar mai karfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowacce rana ta fara fitar da fetur a bara, jiragen ruwan da ke ɗaukar man na zuwa Yammacin Afirka ne. A yanzu jirgin ruwan Mercuria zai tafi Asia a ranar 22 ga Yuni.
“Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Mai saye na da haƙƙin kai wa duk inda yake so,” in ji kakakin matatar mai ta Dangote.
Matatar man ta dala biliyan 20 da da maikudin Afirka Aliko Dangote ya samar a wajen birnin Legas, ta fara aiki a watan Janairun shekarar da ta gabata. Matatar ta fuskanci kalubale da dama.