AFIRKA
1 minti karatu
Cacar-bakin da Mali da Aljeriya ke yi abin damuwa ne — ECOWAS
Kwanan nan ne dai cacar baka ta kaure tsakanin Mali da Aljeriya kan zargin da Mali ta yi na cewa Aljeriya ta kakkaɓo jirgi mara matuƙinta.
Cacar-bakin da Mali da Aljeriya ke yi abin damuwa ne — ECOWAS
Ecowas ta yi kira ga ƙasashen Mali da Aljeriya su yi amfani da tsare-tsare na yanki da na nahiya wajen warware matsalolinsu. / TRT Afrika Français
10 Afrilu 2025

Ƙungiyar Raya Tattalin Aziƙin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana damuwa dangane da yadda dangantaka tsakanin ƙasashen Mali da Aljeriya ta yi tsami.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba a shafinta na X, hukumar ta ECOWAS ta ce cikin damuwa ne take bibiyar cacar-bakan da ake yi tsakanin ƙasar Mali da Aljeriya ta saƙonnin sanarwar da suke fitarwa cikin ‘yan kwanakin nan.

“A madadin ƙasashe mambobin ƙungiyar ECOWAS, hukumar ta bayyana damuwarta matuƙa game da yanayin,” in ji ECOWAS.

 “Tana kira ga Mali da Aljeriya su rage tashin hankali su rungumi tattaunawa tare da amfani da tsare-tsaren yanki da na nahiya domin warware matsalolinsu,” in ji sanarwar.

Kwanan nan ne dai cacar-baka ta kaure tsakanin Mali da Aljeriya kan zargin da Mali ta yi na cewa Aljeriya ta kakkaɓo jirgi mara matuƙinta.

Aljeriya ta rufe sararin samaniyarta ga Mali bisa abin da ta kira “keta doka a-kai-a-kai” bayan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar sun yi wa jakadunsu kiranye daga Aljeriya bayan da aka kakkaɓo jirgin sama mara matuƙin Mali ɗin.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us