Wasu ‘yan bindiga da ke cikin ƙananan jiragen ruwa sun buɗe kan wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa a Bahar Maliya ta hanyar harba masa makamin roka na RPG da kuma amfani da bindiga, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
‘Yan bindigan sun kai harin ne a ranar Lahadi a wani wuri da ke da nisan kilomita 94 daga tashar jiragen ruwa ta Hodeida ta Yemen, kamar yadda Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci na Teku ta Birtaniya (UKMTO) ta bayyana.
UKMTO, wacce rundunar sojin ruwa ta Royal Navy ta Birtaniya ke kula da ita, ta ce:
"Jirgin ya gamu da hare-hare daga ƙananan jirage masu yawa inda aka buɗe masa wuta da bindigogi da kuma rokokin RPG. Tawagar tsaron jirgin ta mayar da martani ta hanyar buɗe wuta kuma har yanzu lamarin na ci gaba."
Kamfanin tsaro na Ambrey da ke Birtaniya ya bayyana cewa jirgin kasuwancin "ya gamu da hari daga ƙananan jirage takwas yayin da yake tafiya zuwa arewa a cikin Bahar Maliya," inda suka yi amfani da bindigogi da rokokin RPG wajen kai harin.
Tashar jiragen ruwa ta Hodeida na ƙarƙashin ikon mayaƙan Houthi da Iran ke mara wa baya, kodayake ba wanda ya ɗauki alhakin wannan harin har yanzu.
Tun a cikin watan Nuwamba 2023, bayan ɓarkewar yakin Isra’ila da Hamas a Gaza, Houthi suka fara kai hari kan jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra’ila a Bahar Maliya da mashigar ruwa ta Aden
Daga baya, a cikin watan Janairu 2024, sun faɗaɗa hare-haren zuwa kan jiragen da ke da alaƙa da Amurka da Birtaniya, bayan da ƙasashen biyu suka fara kai musu hare-hare ta sama.
A watan Mayu, ƙungiyar Houthi ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka, amma ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra’ila a Bahar Maliya, duk da ta amince da yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen hare-haren sama daga Amurka na tsawon makonni.