Iran ta harba daruruwan makaman roka masu linzami zuwa Isra'ila, abin da ya haifar da karin tashin hankali mai tsanani. Kafofin watsa labarai na Iran sun bayyana cewa an samu nasarar kai hari kai-tsaye Tel Aviv, inda aka ga wuta tana tashi kusa da wuraren soji masu muhimmanci, ciki har da cibiyar Ma'aikatar Tsaro, kamar yadda kafofin watsa labarai na Isra'ila suka ruwaito.
Wannan hari na ban mamaki da aka kai a ranar Juma'a da daddare, wanda kafafen watsa labarai na gwamnati a Iran da kuma Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) suka tabbatar, shi ne mafi girman hari kai-tsaye da Tehran ta taɓa kai wa Isra'ila har zuwa yanzu.
Gidan talabijin na Iran, Press TV, ya bayyana cewa "matakin farko" na harin makaman ya yi "tasiri kai-tsaye" a Tel Aviv, yayin da tashar talabijin ta Isra'ila, Channel 13, ta tabbatar cewa an kasa daƙile da dama daga cikin makaman, wanda ya sa suka faɗa wurare daban-daban a kasar.
Wani dan jarida na AFP da ke Tel Aviv ya bayyana yadda hayaki mai kauri ya tashi sama a cikin birnin yayin da fashe-fashe suka rika karaɗe cikin dare. An ruwaito wuta tana tashi kusa da manyan gine-ginen gwamnati da na tsaro, yayin da tawagogin gaggawa suka yi ƙoƙarin shawo kan ɓarnar.
IRGC ta fitar da wata sanarwa tana cewa ta "kai hare-hare kan wurare da dama a Isra'ila," yayin da wani babban jami'in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa: "Babu wani wuri a Isra'ila da zai kasance cikin aminci, ramuwar gayya za ta kasance mai raɗaɗi."
Sojojin Isra'ila sun tabbatar da cewa fashe-fashen da aka ji a faɗin ƙasar sun haɗa da nasarar daƙile wasu makaman da kuma tasirin wasu da suka kai hari. Ba a samu cikakken bayani kan waɗanda suka rasa rayukansu ko girman barnar ba a lokacin da aka fitar da rahoton.
Harin ya biyo bayan kalaman Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya yi alkawarin ɗaukar matakin ramuwar gayya mai tsanani, yana mai cewa Isra'ila ce ta fara wannan yaƙin. "Isra'ila ta fara wannan yaƙi. Za mu ɗauki matakin ramuwar gayya mai raɗaɗi," in ji Khamenei a cikin wani jawabi da aka naɗa tun farko.
Wannan hari ya zo ne bayan jerin hare-haren da Isra'ila ta kai Iran tun daga tsakar daren Juma'a, inda Tel Aviv ta bayyana cewa tana kai hari kan wuraren da suka shafi dabarun tsaro da makamashin nukiliya.