AFIRKA
1 minti karatu
An rantsar da Janar Tiani a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na Nijar na shekara biyar
Kazalika an ɗaga martabar Abdourahamane Tiani daga muƙamin Birgediya Janar zuwa Janar, wanda shi ne muƙamin soji mafi girma a Jamhuriyar Nijar
An rantsar da Janar Tiani a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na Nijar na shekara biyar
An rantsar da Janar Tiani a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na Nijar na shekara biyar / Others
26 Maris 2025

A ranar Laraba ne aka rantsar da shugaban mulkin sojan Nijar Abdourahamane Tiani a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar.

Wani babban jami'in gwamnati ya ce Tiani zai jagoranci al'ummar ƙasar tsawon shekaru biyar har zuwa miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.

An rantsar da Janar Tiani ne a karkashin wata sabuwar yarjejeniya da ta maye gurbin kundin tsarin mulkin kasar ta Yammacin Afirka.

Matakin ya yi fatali da yunƙurin da kungiyar ECOWAS ta yi a yankin na gaggauta dawo da mulkin dimokuradiyya bayan juyin mulkin 2023.

Wa’adin miƙa mulkin na shekaru biyar ya fara aiki ne daga ranar Laraba, a cewar Mahamane Roufai, Sakatare-Janar na gwamnati.

Yana magana ne a wani biki da aka gudanar a Yamai babban birnin kasar inda aka amince da sabuwar yarjejeniyar miƙa mulki da wani taron kasa da aka gudanar kwanan nan ya ba da shawarar.

Kazalika an ɗaga martabar Abdourahamane Tiani daga muƙamin Birgediya Janar zuwa Janar, wanda shi ne muƙamin soji mafi girma a Jamhuriyar Nijar

Wannan ƙarin girma ya ƙara tabbatar da ƙarfin ikon Tiani tun watan Yunin 2023 lokacin da ya jagoranci sojojin da suka hamɓarar da zababbiyar gwamnatin kasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us