RAYUWA
6 minti karatu
Kallo cikin hotuna: Magance samar da hotunan da suka saɓa wa doka
Idan mai daukar hoto bai kula sosai ba, yana iya fadawa hatsarin mamayar surori, ya warwatsa manufofin mulkin mallaka da danniya zuwa hotunan zamani da ake amfani da su a kungiyoyin lafiya, ayyukan jin kai da tallafi na duniya.
Kallo cikin hotuna: Magance samar da hotunan da suka saɓa wa doka
Images hold power which can impact how individuals perceive themselves and how viewers see the photographed. / Getty Images
14 Maris 2025

Daga Ayan Hag Hersi

Mai daukar hoto daga Arewacin Duniya da ke da ingantaciyar na’urar daukar hoto na zuwa Kudancin Duniya da manufar dakko matsalolin lafiya da jama’ar yankin ke fuskanta.

Ana amfani da hotunan da mai daukar hoton ya dauka a kungiyoyin kula da lafiya na duniya da ma na bayar da agajin jin kai da suke dogaro dungurungum kan hotunan don adanawa da shirya bayanai, barkewar annoba da rikici da kuma don ayyukan kungioyin.

Amma kuma hotunan na iya zama wadanda suka saba doka kuma za su iya janyo rashin daidaiton da dole ne a magance shi.

Magance burbushin mulkin mallaka

Marubuci dan kasar Kenya kuma malamin jami’a Ngugi wa Thiong’o ya tattauna kan batun kaward mulkin mullaka a yaruka.

Ya nusar da ra’ayinsa ga marubutan Afirka, inda ya tunkari kalubalen da suke fuskanta wajen amfani da yaruka daban-daban, kamar Turancin Ingilishi da Faransa, da sauran su sama da yarukansu na asali.

Ya bayyana cewa amfani da yarukan Afirka na da babbar rawar takawa a raya al’adun kasa, tarihi da kamanni.

Haka kuma, ina muhawarar cewa kamar yadda yake game da harshe, hotuna ma na da babbar rawa a al’adun kasa, tarihi da kamanni.

A yayin daukar hotuna, mutum na mayar da hankali kan abin da yake dauka tare da tsara bayani, labari ko sako don yada wa da rarrabawa.

Bayanin, labarin ko sakon, tare da hotunan za su zama ‘jakada’ da ke bayyana mutum ko wani abu da aka sdauka hoto.

A saboda haka, hotuna, na da karfin yin tasiri kan yadda daidaikun mutane suka fahimci kawunansu da yadda mutane suke kallon wanda aka dauka hoto. Wannan kuma na saka wanda aka dauka a wata siffa ta alakantuwa da duniya.

Idan mai daukar hoto bai kula sosai ba, yana iya fada wa hatsarin mamayar surori, ya warwatsa manufofin mulkin mallaka da danniya zuwa hotunan zamani da ake amfani da su a kungiyoyin lafiya, ayyukan jin kai da tallafi na duniya.

Magance amincewa, alaka da ka’idoji

A yayin da aka dauki hoto da neman yarda da duba muhimmancin daraja da alaka, hakan na da muhimmanci.

Saidu Abdurrahman ya dauki ragamar wayar da kan jama’a kan daukarb hoto a Nijeriya.

Hotunan da da ke nuna wasu mutane da aka sani a yanayin da suke da ba za su so a gani ba ko yanayin da zia iya zubar musu da daraja, ko yanayin rashin lafiyar muhalli ko wani ibtila’i ko dukka biyun, kuma aka buga su a duniya inda jama’a da dama za su, na kuntatawa mutane da zaluntar su.

Irin wadannan hotuna na kawo tambayar ko an samu yardar su kafin a dauki hotunan ko kuma a’a.

Domin duba hakan, wasu masu bincike kan lafiya sun gudanar da bincike dacewa da girmamawa ga hotunan da aka buga a rahotannin ;lafiya na duniya.

Sakamakon nazari da natijar da aka samu, malaman sun samar da tsarin aiki mai kyau bisa sharudda hudu: shaidar aminta, alakar hotunan da rahoton, gaskiya da girmamawa ga mutane da adadalci da daidaiton wadanda aka dauka hoiton.

Kazalika, kungiyon kasa da kasa da dama sun fitar da dokoki da ka’idojinsu na daukar hotuna.

Daya daga cikin ka’idojin shi ne na Kawancen Kunfiyoyin Hadin Kan Tallafi da Cigaba (CONCORD).

Kundin ka’idojin ya bayyana fitar da hoto na gaskiya, kare muzantawa da girmama zabin mutane wajen kamantawa da suaran batutuwa.

Ba dole ne a koyaushe a yi aiki da wadanna ka;idoji ba, duk da yadda aka amince da bukatar girmamawa, yarda da kare mutunci da kuma daidaito.

Habaka dakokin adalci a ayyuka

A inda kungiyoyi suka saka ka’idojin daukar hoto, alhakin mai daukar hoton ne ya yi aiki da ka’idojin.

Sai dai kuma, masu daukar hoton ba su da hurumi ko ikon juya yadda za a yi aiki da hotunan da yada su.

A saboda haka, kungiyoyi na da alhakin habaka aiki da ka’idojin daukar hoto inda masu dab’i, masu sadarwa da edotoci za su yi aiki da kundin dokokin.

Sani, wanda ya yi aiki a matsayin dan jarida mai daukar hoto ga gidajen jaridu irin su Daily Trust, Leadership, ya ce '“Ina son zuwa daukar wasu wuraren da yadda suke rayuwa”.

Mai daukar hoto na yanke hukuncin wadanne abubuwa ne suka cancanta ya dauka kuma wadanne ne ne za a iya yada su.

Asali, su ne wadanda ya zama dole su tabbatar da an dauki hotuna da yardar mutanen da ake dauka, ana kare mutuncinsu.

A yayin da aka nemi yardar mutanen da ake dauka hoto, za a aje su a matsayin shaida ga kungiyar.

A wannan yanayi, kungiyoyi da masu daukar hoto na aiki tare don tabbatar da aiki da dokokin dauka da dab’i.

Dadin dadawa, masu daukar hoto ne ya kamata su bayar da batu na gaskiya cikin hotuna.

Masu daukar hoto da ke aiki da dokoki d aka’idoji na bayar da bayanan hoto tare da hotunan da suka dauka, suna bayanin yanayin da ake ciki, da ma mutanen da aka dauka hoto. Sai su kuma tabbatar kare martaba da mutuncin mutanen.

Wata hanyar bayyana lamari yadda ya kamata shi ne daukar masu daukar hoto na yankin da suke aiki. Ta hanyar hadin kai da mutanen yankin da daukar hayar kwararru na yankin da ke shaida me ke faruwa, za a samu ilimi, bayanai da karin haske game da hotunan.

A littafinsa, ‘The Foreign Gaze’ Seye Abimbola ya rubuta cewa “….kallon kasashen waje da ke sake fasalin tsayuwarmu da abinda muke iya gani ko fada’, saboda haka, kwararru a yankunan ne za su kula da yadda za a tabbatar da an nuna komai yadda yake.

Hoto babban jigon bayar da bayanai ne. Kamar yadda aka ambata, kuma ta tunanin malamin jami’a na Kenya Ngugi wa Thiong’o, hoto na da babbar rawar taka wajen bayyana al’adun kasa, tarihi da kamanninsu.

 Amfani da hotuna ba bisa ka’ida da adalci ba na kai wa ga malkwada bayanai da suke dakile kamanni da mutuncin kasa.

Marubuciya, Ayan Hag Hersi, ‘yar jarida kuma mai bincike. A baya ta yi aiki da BBC, WHO da SIPRI. Tana rubutu game da ayyukan lafiya a duniya.

Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba lallai ba ne ya zo daidai da ra'ayi,hange da manufofin editan TRT Afrika.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us