GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Shugaban Iran ya ba da umarnin dakatar da hulɗa da hukumar IAEA mai hana yaɗuwar makamin nukiliya
Masoud Pezeshkian ya amince da dokar da tilasta wa gwamnati ta dakatar da hulɗa da hukumar, in ji rahotanni daga ƙasar.
Shugaban Iran ya ba da umarnin dakatar da hulɗa da hukumar IAEA mai hana yaɗuwar makamin nukiliya
Shugaban Iran ya yi shelar dakatar da hulɗa da hukumar IAEA / AP
2 Yuli 2025

Shugaban Iran President Masoud Pezeshkian ya yi shela ranar Laraba cewa ƙasarsa ta dakatar da hulɗa da hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya ta IAEA, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar Press TV da kuma kamfanin dillancin labaran ƙasar Mehr ya ruwaito.

Kazalika kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda gwamnati ke da hannu a ciki shi ma ya ce shugaban ƙasar ya amince rattaɓ hannu kan dokar da ta tilasta wa gwamnati dakatar da hulɗa da IAEA.

A makon jiya, majalisar dokokin Iran ta amince da ƙudirin dakatar da hulɗa da IAEA.

Matakin na zuwa ne bayan dangantaka ta yi tsami tsakanin Tehran da hukumar MDD da ke sa ido kan nukiliya game da damar sa ido da kuma bayyana gaskiya bayan ƙasar ta yi arangamar soji da Isra’ila da Amurka kwanan nan.

Yaƙin kwana 12 tsakanin Isra’ila da Iran ya ɓarke ne ranar 13 ga watan Yuni a lokacin da Isra’ila ta ƙddamar da hare-haren sama kan wuraren nukiliya da sojin Iran.

Tehran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami da jirage mara matuƙa yayin da Amurka ta kai hare-haren bambamai kan tashoshin nukiliyar Iran uku.​​​ Rikicin​​​ ya tsaya ne a ƙarƙashin .

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us