GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Mahama na son Ministocin Kuɗi da Makamashi su sa ido kan tasirin rikicin Isra'ila da Iran kan Ghana
Ya ce duk da ayyukan da gwamnatin ƙasar ta yi na daidaita tattalin arziƙin ƙasar, Ghana ba ta da kariya daga tasirin abubuwan da ke faruwa a duniya.
Mahama na son Ministocin Kuɗi da Makamashi su sa ido kan tasirin rikicin Isra'ila da Iran kan Ghana
Shugaba John Mahama ya ce yaƙin da ake yi tsakanin ƙasashen Isra'ila da Iran ya sa farashin mai ya tashi sosai / Others
17 Yuni 2025

Shugaban ƙasar Ghana, John Mahama, ya umarci Ministocin Kuɗi da na Makamashi na ƙasar su sa ido kan yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da Iran da kuma irin tasirin da zai yi kan fannin makamashin ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a wajen hawan daba na sarakuna da mutane na Jihar Savannah inda ya je rangadin godiya.

Ya ce duk da ayyukan da gwamnatin ƙasar ta yi na daidaita tattalin arziƙin ƙasar, Ghana ba ta da kariya daga tasirin abubuwan da ke faruwa a duniya.

Kamfanin dillancin labaran ya ambato shugaban yana cewa: “Lamuran da ke faruwa a Gabas Ta Tsakiya waɗannda suka haɗa da musayar wuta da makamai masu linzami tsakanin Isra’ila da Iran sun fara tayar da farashin ɗanyen mai sosai.”

“Na buƙaci Ministan Kuɗinmu da Ministan Makamashinmu su sa ido sosai kan lamarin kuma su yi gwaji game da irin tasirin da zai iya yi kan farashinmu na mai kuma su tsara matakai domin kare nasarorin da muka yi kwanan nan,” in ji shugaban.

Ƙasar Ghana tana samar da ɗanyen mai yayin da ƙasar take shigowa da tataccen man fetur daga ƙetare.    

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us