A ranar Alhamis ɗin ne alhazan musulmai suka yi sallah a saman dutsen Arafat a daidai lokacin da akai gudanar da Aikin Hajjin bana, kana hakan na zuwa ne a lokacin da mahukuntan Saudiyya suka yi kira ga maniyyatan su guji fita waje a lokacin yanayi mafi zafi na rana.
Dubban alhazai ne suka fara taruwa kafin fitowar alfijir a kewayen tsaunin da filin na Arafat inda ake kyautata zaton Manzon Allah SAW ya yi hudubarsa ta karshe.
Yayin da wasu suka iso da wuri domin cin gajiyar wannan safiya mai sanyi, dauke da laima masu launi iri daban-daban, maniyyata da dama za su zauna na tsawon sa'o'i suna addu'o'i da karanta Ƙur'ani har zuwa maraice, a kololuwar yanayi mai wahala na Aikin Hajji.
Bayan faduwar rana, za su nufi Muzdalifah, wani waje da ke tsakanin filin Arfa da ‘‘filin tantuna’’ na Mina, inda za su tattara tsakuwowin da za su yi “jifan shaidan” da su.
"Wannan wani abu ne da na saba gani duk shekara a talabijin a lokacin Aikin Hajji kuma a ko yaushe ina da burin cewa: 'Allah Ya sa na zo nan," in ji wani Alhaji daga Pakistan mai suna Ali mai shekaru 33, daya daga cikin alhazai miliyan 1.5 da suka isa Saudiyya don sauke Aikin Hajji na bana.
"Na yi ta ƙoƙarin zuwa nan... kusan tsawon shekaru uku da suka gabata," a cewar Ali yayin da yake tsaunin. "Ina ji tamkar samu komai.’’
Daruruwan alhazai sanye da fararen kaya ne suka mamaye saman kan dutsen, tare da wasu da dama a kasa suna addu'a.
A farkon makon nan ne mahukuntan Saudiyya suka yi kira ga maniyyata da su kasance a cikin tantunansu tsakanin karfe 10:00 na safe zuwa karfe 4:00 na maraicen ranar Alhamis, lokacin da rana ta fito ta kuma fi tsananin zafi.
An ajiye fankoki ta ko ina don samar da iska da sanyi a kasan dutsen.
Yanayin zafi na wannan shekara ya wuce ma'aunin Celsius 40 (104 Fahrenheit) a lokacin Aikin Hajji da ke zama daya daga cikin manyan tarukan addini na duniya na shekara-shekara, wanda ya hada maniyyata daga sassan duniya, da za su sauke farali.
'Babban mafarki ne'
Jami’ai sun ƙara ƙaimi wajen kokarin rage zafin don kauce wa sake faruwa yanayin da aka fuskanta a aikin hajjin bara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mahajjata 1,301 yayin da yanayin zafi ya kai ma’aunin maki 51.8C.
"Na zo nan da wuri don guje wa rana, daga baya kuma zan yi addu'a a cikin tantina," in ji Adel Ismail, mai shekara 54, daga Siriya.
Domin samar da tsaro a Aikin Hajjin bana, hukumomi sun samar da ƙarin kayayyakin more rayuwa, tare da tura karin dubban ma’aikata tare da dogaro kan kayan aikin fasaha na zamani don taimaka wa wajen takaita cunkoson jama’a.
Mahukunta kasar Saudiyya sun tattara fiye da hukumomin gwamnati 40 da jami’ai 250,000, tare da ninka kokarinsu na yaƙi da cututtuka masu nasaba da zafi biyo bayan mummunan yanayi zafi da aka fuskanta a 2024.
An faɗaɗa wurare masu inuwa da murabba'in mita 50,000 (kadada 12), kana dubban likitocin za su kasance cikin shirin ko ta kwana, sannan za a tura sama da na'urorin samar da sanyi sama da 400, in ji Ministan Aikin Hajji.
Cikin yanayi na kukan farin ciki Iman Abdel Khalek ta ce ta shafe shekaru 10 tana son sauke farali, kuma ta shiga cikin sauki a lokacin da ta isa filin Arafat.
"Cikar babban buri ne na tsawon shekaru," kamar yadda matar mai shekaru 50 ta fada daga kasan dutsen na Arfa.
Hukumomi sun ce akasarin wadanda suka mutu a shekarar 2024 na daga cikin mahajjatan da ba su yi rajista ba wadanda ba su da damar samun ababen more rayuwa kamar tantuna masu samar da sanyi da kuma motocin safa-safa.
A bana, hukumomi sun daƙile shigowar mahajjata wadanda ba su yi rajistar shiga Makka ba, inda ake samame akai-akai, da sa idon jirage masu saukar ungulu da kuma yawan wayar da kan jama’a.
Ana ba da izinin Aikin Hajji ga ƙasashe bisa ƙa'ida kuma ana rarraba wa daidaikun mutane ta hanyar cancanta.
Kuma ko ga wadanda suka samu wannan dama, tsadar kudin biya kan sa mutane da dama yunƙurin zuwa Aikin Hajji ba tare da neman izini ba, duk da cewa suna fuskantar barazanar kame da fitar da su daga kasar idan aka kama su.
Saudiyya na samun biliyoyin daloli a kowace shekara daga Aikin hajji, da kuma Umrah, wanda ake yi a wasu lokutan cikin kowacce shekara.