A ranar Juma’a China ta tabbatar da batun ƙulla wata yarjejeniyar kasuwanci da Amurka, tana mai cewa Washington za ta ɗage "matakan takunkuman da ta ƙaƙaba" yayin da ita kuma Beijing za ta yi "bita tare da amince wa" kan abubuwan da ke ƙarƙashin ikon fitar da kayayyaki.
"Ana fatan Amurka da China za su haɗu a tsakiya," kamar yadda kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar ta China ya bayyana a cikin wata sanarwa.
A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar da cewa bangarorin biyu sun cim ma matsaya kan batutuwan da suka haɗa da gaggauta jigilar wata ƙasa da ba a fiye samunta ba zuwa Amurka.
Bayan tattaunawar da aka yi a Geneva a watan Mayu, Washington da Beijing sun amince da rage harajin bani gishiri in baka manda kan kayayyakin juna na wani ɗan lokaci.
China ta kuma ƙudiri aniyar sassauta wasu matakan da ba na haraji ba, amma daga baya jami'an Amurka sun zargi Beijing da keta yarjejeniyar da kuma jinkirin amincewa da lasisin fitar da albarkatun ƙasa.
A ƙarshe dai ɓangarorin biyu sun amince da wani tsari da ciyar da yarjejeniyarsu ta Geneva gaba bayan tattaunawar da suka yi a birnin Landan a wannan watan.
Wani jami'in fadar White House ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a ranar Alhamis cewa, gwamnatin Shugaba Donald Trump da China sun "amince da ƙara fahimtar tsarin aiwatar da yarjejeniyar Geneva".
Wannan ƙarin bayanin ya biyo bayan Trump ya shaida wa wani taro cewa Washington ta ‘‘sanya hannu’’ yanzu a kan wata yarjejeniya da ta shafi kasuwanci da China, ba tare da ya yi wani ƙarin bayani akai ba.
Kazalika, Beijing ta tabbatar a yau Juma'a cewa an cim ma matsaya.
"Bayan tattaunawar London, ɓangarorin biyu sun ci gaba da tuntuɓar juna," in ji kakakin ma'aikatar kasuwanci.
"Bangarorin biyu a kwanan nan sun ƙara tabbatarwa tare da bayyana cikakkun bayanai game da tsarin," inda suka ƙara da cewa, China za ta yi nazari tare da amincewa da tsarin fitar da kayayyaki waɗanda suka cika ka'idoji kamar yadda doka ta tanada.
"Ɓangaren Amurka dai zai soke jerin matakan takunkumai kan China."
"Muna fatan ɓangaren Amurka zai yi aiki tare da China, bisa muhimman shawarwari da buƙatun da aka gabatar yayin tattaunawar da shugabannin ƙasashen biyu suka yi a ranar 5 ga watan Yuni," in ji kakakin a cewar jaridar South China Morning Post.