KASUWANCI
1 minti karatu
Asusun adana zinari na Ghana ya kai ton 31.37 a watan Afrilun 2025
Sabbin bayanai daga Bankin Ghana sun danganta wannan ci gaba da aka samu da karuwar sayen zinare da nufin karfafa asusun ajiyar waje da kuma bunkasa tattalin arziki.
Asusun adana zinari na Ghana ya kai ton 31.37 a watan Afrilun 2025
Ghana's wildcat gold mining booms, poisoning people and nature / Reuters
7 Mayu 2025

Asusun adana zinare na Ghana ya bayyana ƙarin da aka samu na zinare a watan Afrilun 2025 na tan 31.37, sama da ton 31.01 da aka samu a watan Maris kana sama da ton 8.78 a watan Mayun 2023.

Sabbin bayanai daga Bankin Ghana sun danganta wannan ci gaba da aka samu da ƙaruwar sayen zinare da nufin ƙarfafa asusun ajiyar waje da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Ta hanyar ƙara yawan hannayen jarinsa na Zinare, Babban Bankin ya ƙuduri aniyar rage dogaro da kudaden waje da kuma karkata zuwa sauran albarkatun kasa.

A matsayinta na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da zinari a Afirka, Ghana ta mayar da hankali wajen bunƙasa ƙananan masana'antun haƙar ma'adinai.

Haka kuma, bankin na Ghana ya ƙulla yarjejeniya mai kƙrfi tare da wasu manyan kamfanonin haƙar ma'adinai tara, inda aka ba su damar samar da kashi 20 na zinaren da suke haƙowa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us