DUNIYA
2 minti karatu
Amazon da Meta za su ba da gudunmawar dala miliyan ɗaɗɗaya ga asusun shirin rantsar da Trump
Wani mai magana da yawun Amazon ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis inda ya ce kamfanin zai kuma yada bikin rantsar da Trump a shafukansa na intanet ta bidiyo.
Amazon da Meta za su ba da gudunmawar dala miliyan ɗaɗɗaya ga asusun shirin rantsar da Trump
Amazon da Meta za su ba da gudunmawar dala miliyan ɗaɗɗaya kowanne ga asusun rantsar da Trump / AFP
13 Disamba 2024

Kamfanin Amazon na shirin bayar da gudunmawar dala miliyan daya ga zababben shugaban kasa Donald Trump don shirin rantsar da shi, matakin da ya zo a daidai lokacin da manyan kamfanonin fasaha ke kokarin kyautata alakarsu da shugaban kasar mai jiran gado.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis inda ya ce katafaren kamfanin na intanet zai kuma yada bikin rantsar da Trump a shafukansa na intanet ta bidiyo baya ga  gudunmawar da ta kai dala miliyan 1.

Tun da farko dai, Meta, babban kamfanin Facebook da Instagram, ya ce ya ba da gudunmawar dala miliyan 1 ga asusun rantsar da Trump.

Jaridar Wall Street Journal ce ta fara ba da rahoton tsare-tsaren Amazon. Rahoton ya zo ne bayan da Trump ya fada da safiyar Alhamis cewa wanda ya kafa kamfanin, Jeff Bezos, na shirin kai masa ziyara a mako mai zuwa.

Mutanen biyu sun samu sabani a baya. A lokacin wa'adinsa na farko, Trump ya soki Amazon kuma ya yi adawa da labaran siyasa a Washington Post, wanda Bezos ya mallaka.

Shi ma kuma Bezos ya soki wasu kalaman Trump na baya. A cikin 2019, Amazon kuma ya yi jayayya a shari'ar kotu cewa nuna son kai ga kamfanin ya cutar da damarsa ta cin nasarar kwangilar dala biliyan 10 ta Pentagon. Daga baya gwamnatin Biden ta bibiyi wata kwangila tare da Amazon da Microsoft.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us