Turkiyya za ta haɗa ƙasashen Afirka bakwai zuwa Aikin Hanyar Ci-gaba da kuma Hanyar Kasuwanci ta Tsakiyar Hanyar ta hanyar yarjeniyoyin fahimtar juna da aka sanya wa hannu kwanan nan a wani taron sufuri da aka gudanar a Istanbul.
Ministan Sufuri da gine-gine na Turkiyya, Abdulkadir Uraloglu, ya bayyana a wata sanarwa cewa, Taron na Haɗa Hanyoyin sufuri na Duniya ya samu halartar jami'ai daga Burkina Faso, da Jamhuriyar Kongo, da Djibouti, da Ethiopia, da Ghana, da Guinea, da Maroko, da Somaliya, da Mauritania, da Laberiya, da Namibiya, da Ivory Coast, da kuma Masar.
Taron ya gudanar da wani zama na musamman da aka keɓe don haɗa Afirka da hanyoyin zirga-zirga na duniya.
"Bayan zaman, mun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna kan haɗin gwiwa wajen ƙarfafa alaƙar sufuri da ƙasashe bakwai na Afirka, wato Mauritaniya, da Somaliya, da Jamhuriyar Kongo, da Djibouti, da Laberiya, Guinea, da Ghana," in ji shi.
Za a haɗa nahiyar Afirka cikin Aikin Hanyar Ci-Gaba ta hanyar Tekun Fasha da hanyar Kasuwanci ta Tsakiyar da ake bi ta Turkiyya.
“Za mu tabbatar da cewa an samu hanyoyin shiga wuraren kasuwanci na duniya daga Afirka ba tare da katsewa ba, kuma waɗannan hanyoyin za su sauƙaƙa haɗewar Afirka kai-tsaye cikin tsarin kasuwanci da ya taso daga Asiya zuwa Turai,” in ji shi.