AFIRKA
5 minti karatu
Babban tasirin yakin Sudan kan tsarin ilimin kasar
Wasu hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun tattara bayanan babban tasirin da yakin Sudan ya yi kan tsarin ilimin kasar.
Babban tasirin yakin Sudan kan tsarin ilimin kasar
Tasbih is among 19 million children in Sudan who have been forced to flee for safety, leaving school behind.
21 Maris 2025

Tun bayan barakewar rikicin a watan Afrilun 2023, kimanin yara miliyan 19 sun daina zuwa makaranta a Sudan.

Tasirin ya yi matukar muni a bangaren kayan more rayuwa da daidaikun jama’a inda kashi 90 na yara kanana suka daina zuwa makaranta.

Bayanin matsalar

Manyan matsalolin da rikicin ya haifar, tsananin rashin cigaban ilimi, da rushewar kayan more rayuwa, da rashin bayar da fifiko ga ilimi da koyon sana’o’i, musamman ga yara mata, za su ci gaba da tasiri kan zaman lafiya da kwanciyar hankalin Sudan.

A 2023, yawan jama’ar Sudan ya kai miliyan 43 inda kasha 40 nasu kuma ‘uan aksa da shekaru 15 ne.

Ana sa ran yawan jama’ar Sudan zai karu zuwa mutm miliyan 75 nan da 2043 inda kimanin kasha 33 za su kasance ‘yan kasa da shekara 15.

Gamayyar tasirin ilimi d ayawan jama’a, tare da tabarbarewar al’amura, za su yi mummunar illa ga makomar kasar.

Daduwar shekarun aiki gami da raguwar damarmakin aikin tare da lalacewar ingancin tsarin ilimi, hakan zai kai ga mutuwar kasar matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba a gajere da matsakaicin lokaci.

Matsalolin da yakin ya janyo

Tun kafin fara yakin ma, da ma yanayin koyo da koyarwa a SUdan ya shiga halin inna naha.

Zanga-Zanga da tayar da zaune tsaye da aka gudanar sun janyonrufe makarantu manya da kanana na tsawon watanni a wancan lokacin. An yi kiyashin cewa sama da yara kanana miliyan 3.6 (‘yan shekaru 5 zuwa 13) sun daina zuwa makaranta a tsakanin 2020/2021.

Rashin isassun kudade da kayan aiki a bangaren kayan more rayuwa na da koyo da koyarwa, da jin dadin malamai ma kalubale be da ke tasiri wajen samar da ingantaccen ilimi a kasar.

Wannan nafaruwa ne saboda, a matsakaicin ma’auni, Sudan na kashe kashi 9 cikin dri na kasafin kudinta ga Ilimi, idan aka kwatanta da na sauran kasashen Afirka inda ake kashe wa ilimi kusan kashi 17.

A yayin da ake yi a yanzu, da yadda aka rushe gaba daya ko wani bangare na kayayaki, aka kuma raba dalibai da malamai da matsugunansu, tasirin ya yi tsauri inda makarantu da dama a kasar suka koma wajen fakewar mutane.

‘Yan wurare d ake iya samun ilimi cikin nutsuwa kadan suka rage, wanda ya sanya da wahala mahukunta yankuna da na kasa su dawo bakin aiki don koyarwa a makarantu.

A yayin da shugabannin sashen ilimi a kasar suka yi kokarin ganin an dawo koyo da koyarwa ta hanyar yanar gizo, don a tabbatar da gama jarrabawa, wadannan hanyoyi ba su yi nasara ba duba da bambancin abin hannu wanda ke kara kawo tsaiko ga dalibai da dama wajen samun yanar gizo ko na’’urorin amfani.

Dadin dadawa, a yayin da gine-gine da yanar gizo suka rushe baki daya, an samar da Starlink da suaran su a matsayin sauyi tare da kaliubale da damarmaki.

Hasashe na nan gaba

Tsayayyiyar hanyar auna tarin ilimi a kasa ita ve auna matsakaicin shekarun manya (shekara 15 zuwa sama).

Nazari da bayanai da suka fito daga Cibiyar Nazarin Tsaro da Makomar Afirka na nuna cewa a Sudan, matsakaicin shekarun ilimi a tsakanin manyan shi ne 6. Wannan na nufin nan da 2043 mafi yawancin balagaggu za su kammala ilimin firamare da sakandire.

Sai dai kuma, wannan hasashe ne a ke bisa doron bayan kasa da aka samu kafin a fara yakin.

Bayan baya bayan nan da na yanzu da ke bayani kan sakamakon da aka samu daboda tsugunar da mutane, rusa makarantu ko amfani da makarantun a matsayin wuraren zama d akarancin kayan aiki sun zama manyan matsalolin da ya kamata a magance su.

Wannan zai fara da taimaka wa wajen auna tsananin illar da aka yi da samar da bayanan matakan da aka dauka da kai dauki duba ga makomar yadda za a kawo gyaran.

Yiwuwar yara da matasa da ba sa aiki komkaratu su shiga ayyukan yaki su dauki makamai zai ci gaba da kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan.

Daukar yara kanana a ayyukan soji da shiga kungiyoyin ‘yan tawaye abu ne da ya zama ruwan dare kuma an bayyana damuwa tun farkon fara yakin.

Shawarwari

A wannan lokaci, ya zama wajibi kungiyoyi masu zaman kansu da masu bayar da tallafi da hukumomin majalisar dinkin duniya su duba yadda za su samar da kai dauki nan da nan da kirkirar hanyoyin samar da shirye-shiryen ilimi ga yaran da ke sansanonin ‘yan gudun hijira a Sudan da kasashe makota inda mafi yawan masu gudun hijirar ke zaune.

Wannan zai samu tasiri daga kudaden tallafi da ci gaba da aka bayar kwanakin nan don sake gina tsarin ilimi a Sudan.

Yanzu ya rage na Ma’aikatar ilimi ta Sudan ta hada kai da abokan kasa da kasa don tsara salon koyo da koyarwa ga daliban firamare da makarantun koyon sana’o’i a sakandire da manyan makarantu. Bayar da fifiko ga na farkon zai sanya a cim ma burin nan da 2034 kowanne baligi ya kammala ilimin firamare.

Sake gina kasar na tsawon lokaci bayan yaki zai mayar da hankali ne ga fifita tsarin ilimi.

Ya zama dole a samar da isassun kayan aiki don tabbatar da kowa ya samu damar yin karatu sannan a inganta manhajar kasa duba ga tsarin kasa da kasa da ayyuka masu kyau da tsarin shirye-shiryen ilimi da za su tabbatar da tsallaka wa daga yarinta zuwa samarta da manyanta ta hanyar samar da ma’aikata kwararru da kayan aiki.

Zuba jari a ilimi na da muhimmanci wajen sake gina kasar Sudan da kubutar da makomar yaranta da matasanta.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us