Koriya ta Arewa ta yi Allah wadai da harin tsokana na zaluncin da sojin Isra’ila ke yi kan Iran, tana bayyana shi a matsayin "laifi kan bil’Adama " tana kuma gargaɗin cewa [matakin] na iya janyo babban yaƙi a yankin Gabas Ta Tsakiya inda ake iya samun tashin hankali a ko yaushe.
A wata sanarwar da kafar ƙasar ta KCNA ta watsa ranar Alhamis, wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Koriya ta Arewa ya ce Pyongyang ta bayyana "damuwa sosai " game da hare-haren sojin Isra’ila kan Iraniyawa fararen hula da tashoshin nukiliya da kuma tashoshin makamashi tare da kuma yin "Allah wadai da shi gaba ɗaya."
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce kashe fararen hula da hare-haren Isra’ila suka yi "laifi ne da ya fi ƙarfin yafewa kan bil’adama," kuma ya zargi Tel Aviv da aikata "ta’addancin da ƙasa ta ɗauki nauyinsa " wanda ke ƙara barazanar "wani sabon yaƙi na kowa ina" a yankin.
Koriya ta Arewa ta kuma gargaɗi Amurka da kuma ƙasashen Turai kada su ci gaba da shiga yaƙin.
"Lamari mai hatsari da duniya ta gani a halin yanzu ya tabbatar da cewa Isra’ila, wadda ke samun taimako da goyon bayan Amurka da [Turawan] Yamma, wata aba ce mai kama da kansa ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya kuma babbar ummul haba’isin lalata zaman lafiyar duniya da tsaro ce," in ji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar.
"Ƙasashen duniya na kallon yadda Amurka da muƙarraban Yamma ke ruruta wutar yaƙi, suke ƙin amincewa da ‘yancin kare kai na Iran, wadda aka yi wa ɓarna," in ji shi.
'Mataki na bala’i'
Kalaman Koriya ta Arewa na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce "haƙurinsa ya ƙure" a kan Iran.
Koriya ta Arewa ta nemi Washington ta daina abin da take yi, tana mai gargaɗin cewa matakan da Amurka da ƙawayenta suka ɗauka na "tura yanayin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya zuwa wani mataki na bala’in da ba za a iya shawo kansa ba."