Farashin ɗanyen mai ya yi tashin gauron zabi bayan hare-haren saman da Amurka ta kai kan tashoshin nukiliyar Iran a ƙarshen mako, lamarin da ya janyor fargabar faɗaɗa yaƙi a yankin da kuma yiwuwar katse gudanar makamashi.
Farashin ɗanyen mai samfurin Brent da kuma samfurin WTI sun tashi da fiye da kashi huɗu cikin ɗari.
Barazana ga Mashigin Hormuz
Tashin farashin ya biyo bayan matakin da Amurka ta ɗauka na haɗa kai da Isra’ila wajen kai hare-hare kan tashoshin nukiliyar Iran a Fordow da Natanz da kuma Isfahan, lamarin da ya janyo jerin sabbin barazana daga Tehran ta rufe Mashigin Hormuz — wata muhimmiyar tsukakkiyar hanyar jigilar mai inda kashi ɗaya cikin biyar na man duniya ke bi.
Gidan tabalijin na Iran Press TV ya ba da rahoton cewa majalisar dokokin Iran ta amince da wani ƙuduri da ke goyon bayan rufe mashigin.
Duk da cewa Tehran ta yi irin wannan barazanar a baya, ba ta taɓa aiwatar da matakin ba.
Masharhanta na gargaɗin cewa ko ma ba a rufe mashigin gaba ɗaya ba, ƙarin tashin hankali da kuma barazana ga hanyoyin jigila na ruwa ka iya janyo ƙarin tsadar kuɗin dako da na inshora, lamarin da zai taƙaita fitowar mai daga yankin.
"Barazanar lalata kayayyakin aikin mai sun ƙaru sosai," in ji June Goh, wani babban mai sharhi a kamfanin Sparta Commodities.
"Masu jigila ta jiragen ruwa za su ƙara rage harkokinsu a yankin."
Bankin zuba jari na Goldman Sachs ya ce idan aka rufe wani ɓangare na mashigin Hormuz kawai — lamarin da zai rage rabin man da ke wucewa a ko wane wata — farashin gangar mai samfurin Brent zai iya kai dala $110. Sai dai kuma, a halin yanzu bankin yana tunanin ba za a samu wani gagarumin tsaiko ba.
Farashin samfurin man Brent ya riga ya ƙaru da kashi 13 cikin 100 tun da Isra’ila ta fara ƙaddamar da yaƙinta kan Iran ranar 13 ga watan Yuni, yayin da farashin samfurin WTI ya ƙaru da kashi 10 cikin 100.